Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC
- Jam’iyyar PDP a jihar Yobe ta yi rashin wani jigo mai karfi, Sanata Mohammad Hassan, wanda ya bar ta ya koma wata jam'iyyar
- Sanata Hassan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki da yammacin ranar Talata 1 ga watan Fabrairu
- Wannan ya kasance abin farin ciki ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ciki har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan
Jihar Yobe - Wani fitaccen sanata mai wakiltar Yobe, Sanata Mohammed Hassan, a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP.
Sanata Hassan ta shafin sada zumunta na Facebook ya ce ya dauki matakin ne da yammacin ranar Talata sannan ya ziyarci shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni kan shawarar tasa.
Daya daga cikin magoya bayan Sanata Hassan, Abdullahi Yakubu, a shafukan sada zumunta wanda ya mayar da martani game da ci gaban ya ce jam’iyya mai mulki ta samu dawowar jigonta cikinta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yakubu ya ce:
"APC ta dawo da jigonta da ya bata, ina taya murna da maraba da zuwan mai girma Sanata Mohammed Hassan."
Haka kuma, shawarar Hassan ta kawo farin ciki ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan wanda a shafinsa na Twitter ya rubuta cewa:
"Na ji dadin tarbar Sanata Mohammed Hassan da yammacin yau a gidana, bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC."
Mala Buni ya yi zama da Shekarau da manyan APC da ke fada da Ganduje
A wani labarin, Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni ya hadu da ‘yan tawaren APC na jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Mai Mala Buni ya yi zama da jagororin jam’iyyar ta APC mai mulki na reshen jihar Kano a yammacin Talata a Abuja.
Kawo yanzu ba mu samu labarin matsayar da aka cin ma bayan wannan tattaunawa da aka yi ba.
Majiya ta shaidawa jaridar cewa an yi wannan zama ne da nufin kawo karshen sabanin da ake samu tsakanin manyan ‘ya ‘yan APC da bangaren gwamnati.
Asali: Legit.ng