Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya bayyana sunan wanda zai gaji kujerarsa a 2023
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya sanar da sunan ɗaya daga cikin kwamishinoninsa a matsayin wanda zai gaji kujerarsa
- Gwamnan ya sanar da kwamishinan ƙasa da albarkatun ruwa, Pasto Umo Eno, a matsyain wanda zai zama gwamna na gaba a 2023
- Sai dai ga dukkan alamu hakan bai wa wasu jiga-jigan jiha daɗi ba, musamman masu son takarar gwamna a 2023
Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya ayyana kwamishinan ƙasa da albarkatun ruwa, Umo Eno, a matsayin wanda yake so ya gaje kujerarsa a 2023.
The Nation ta rahoto cewa zaɓin gwamnan ya haddasa rarrabuwar kai a majalisar zartarwa da kuma jam'iyyar PDP reshen jihar, inda mambobi da dama su kai watsi da lamarin.
Gwamna Emmanuel ya faɗi matsayarsa ne ranar Lahadi da daddare a wurin wani taro da ya ƙunshi shugabannni a jihar da kuma masu hanƙoron kujerar gwamna, cikin su harda yan majalisu.
Sai dai wannan sanarwa ta kawo ƙarshen tashin hankali da kuma kace-nace da ake ta yaɗa wa tsawon watanni kan wanda gwamnan zai tsayar ya gaji kujerarsa.
Sabon rikici a majalisar zartarwa ta Akwa Ibom
Rahoto ya nuna cewa wannan cigaban da gwamna ya sanar ya bar baya da ƙura inda wasu daga cikin kwamishinoni dake hanƙoron kujerar gwamna suka yi watsi da lamarin.
Shugaban kwamitin shari'a a majalisar dokokin jihar, Onofiok Luke, wanda ke yunkurin maye gurbin gwamna a 2023, ya fice daga ɗakin taron bayan sanar da magajin gwamnan.
Kazalika wata majiya tace kwamishinoni uku ba su halarci taron ba, kuma an kira taron har gidan gwamnati ba tare da faɗin abinda za'a tattauna ba, kamar yadda Punch ta rahoto.
Shin meyasa gwamnan ya ɗauki wannan matakin?
Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Akwa Ibom, Ekerete Udo, wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, ya ce an ɗauki matsaya ne bisa amincewar masu ruwa da tsaki na kowane ɓangare.
Ya ce:
"Gwamnan ya sanar da cewa Kwamishina Eno ne Allah ya bayyana masa a matsayin gwamna na gaba."
"Kuma tsohon gwamna, Obong Victor Attah, ya gaya wa masu ruwa da tsaki daga kowace mazaɓar sanata uku dake jihar, waɗan da suka yaba da zaɓin"
A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya kuduri aniyar murkushe yan bindiga baki ɗaya kafin wa'adinsa ya ƙare a 2023
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya ce kafin ya miƙa mulki a 2023, sai ya ga bayan yan ta'adda baki ɗaya, zaman lafiya ya dawo.
Buhari wanda ya kai ziyara fadar Sarkin Musulmi a Sokoto , yace abun damuwa ne matauƙa yadda mutanen dake rayuwa tare, suke kashe junan su.
Asali: Legit.ng