Siyasar Kano: Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Rimin-Gado, ya koma PDP
- Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
- Rimin-Gado ya ce ya koma babbar jam'iyyar adawar ne domin yiwa mutane da jiharsa hidima
- Ya kuma ce PDP ce za ta ceto jihar daga fadawa rikicin siyasa
Kano - Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar People Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2023.
Rimin-Gado ya bayyana cewa ya mika takardar neman shiga PDP ta yanar gizo yayin da yake sa ran yin rijista a unguwarsa ta karamar hukumar Rimingado a watan Fabrairu, jaridar Punch ta rahoto.
Tun bayan dakatar da shi da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar 5 ga watan Yulin 2021, fastocin tsohon shugaban na hukumar yaki da cin hanci sun karade unguwanni a Kano inda suke ayyana aniyarsa na takarar gwamna a zabe mai zuwa.
Yayin da wasu daga cikin fastocin suka bayyana babu tambarin kowace jam'iyya, sauran na dauke da tambarin APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma, Magaji ya kauracewa harkokin APC a matakin karamar hukuma da jiha kuma bai hade da kowani bangare ba na tsagin jam'iyyar mai mulki.
Ku tuna cewa a watan Disamban 2021, yan sanda sun dakile wani yunkuri na Rimin-Gado don yin jawabi ga dubban matasa a Kano domin tunawa da ranar yaki da rashawa ta duniya inda suka rufe wajen taron.
Sai dai kuma, da yake magana kan dalilinsa na komawa PDP, Rimingado ya ce ya shiga jam'iyyar adawar ne saboda ita kadai ce za ta ceto jihar Kano daga rikicin siyasar da take ciki a yanzu.
Daily Trust ta kuma rahoto cewa Rimingado ya kara da cewar PDP za ta wanke Kano daga rikicin siyasa a 2023.
“Na yi nazari kan halin da siyasar Kano ke ciki a yanzu kuma na gano cewa da rikicin siyasar cikin gida da ake fama da shi a bangaren Ganduje da Shekarau na jam’iyyar All Progressives Congress, PDP ce kawai madadin jam’iyyar da za ta iya ceto lamarin.
"Batun wanda zai zamo gwamnan jihar na gaba, ko wadanda za su zamo sanatoci a dukkayankunan uku ba shi bane, abun da muke kokarin gani a yanzu shine ceto Kano daga rikicin siyasa. Siyasa ba abar a mutu ko ayi rai bace.
"Na koma PDP ne domin yiwa mutanena da jihar hidima. Na yi hakan a karkashin gwamnatin APC kuma a shirye nake na kara kaimi a karkashin kowace jam'iyyar siyasa."
Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023
A wani labarin kuma, Shugaban cocin superintendent of Glorious Vision World Outreach Ministries, Rev (Dr.) David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya.
A cewar faston, Tinubu na daya daga cikin yan tsirarun mutane da za su iya gyara kasar a matsayin shugaban kasa.
A watan nan ne dai tsohon gwamnan na Lagas ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng