Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP

Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP

  • Gabannin babban zaben 2023, Gwamba Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana matsayinsa a kan yankin da ya kamata ya samar da magajin Shugaba Buhari
  • Mohammed ya ce a iya saninsa a jam'iyyarsa ta PDP, yankin arewa ne ya kamata ya ci gaba da mulki domin shugaba na karshe da jam'iyyar ta yi ya fito daga kudu ne
  • Ya ce yin hakan shine zai zamo adalci da daidaito domin a shekaru 16 da PDP ta yi a mulki, yan kudu ne suka yi jagorancin shekaru 14

Bauchi - Channels TV ta rahoto cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, na kira ga a bari yankin arewacin Najeriya ya ci gaba da rike mulki a 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya hau karagar mulki a 2015 zai kammala wa'adinsa na shekaru takwas a 2023, lamarin da ya haifar da kace-nace a kasar game da yankin da ya kamata ya samar da shugaban kasa na gaba.

Kara karanta wannan

Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA

Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ta samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP
Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ta samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

Koda dai manyan jam'iyyun siyasar kasar na APC da PDP ba su riga sun mika tikitin shugaban kasa ga kowani yanki ba, akwai kiraye-kiraye da ake ta yi kan a mika shugabanci ga kudu.

Sai dai Gwamna Mohammed, wanda ya ce yana sane da kiraye-kirayen, ya ce lallai arewa maso gabas ya kamata a bai wa tikitin shugabancin kasar don daidaito da adalci.

Jaridar The Nation ta nakalto gwamnan yana cewa:

"Ina so na sanar da yan Najeriya musamman masu kira ga a mika shugabancin 2023 ga kudu cewa yanzu zagayen arewa ne ta samar da shugaban kasa na gaba.
"Muna sane da fafutukar yankin kudancin kasar saboda shugaban kasar a yau, Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya fito daga arewa zai kammala wa'adinsa a 2023, don haka a mika mulki zuwa kudu.

Kara karanta wannan

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

"Amma ina son fadin cewa ni a PDP nake, ba a APC nake ba. APC ce ke da wannan nauyi na mika shugabanci zuwa kudi.
"A jam'iyyata, shugaban kasa na karshe shine Goodluck Ebele Jonathan, daga kudu kuma shine shugabana.
"A wannan lokaci, jam'iyyata na kan mulki tsawon shekaru 16; mutanen kudu ne suka yi jagoranci a shekaru 14, don haka ina adalci da hujjar suke?
"Saboda haka, zagayen arewa ne ya samar da shugaban kasa na gaba."

Sauya sheka: Yari da Marafa sun gana da Atiku da Saraki

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya yi wata ganawa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Alhamis, 27 ga watan Janairu.

Hakazalika Sanata Kabiru Marawan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas ma ya kasance a cikin ganawar, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

A yanzu haka, Yari da Marafa suna wakiltan tsagi biyu mabanbanta a jam'iyyar APC reshen Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng