2023: Matasan arewa sun roƙi Ɗangote da Otedola su fito takarar shugabancin ƙasa

2023: Matasan arewa sun roƙi Ɗangote da Otedola su fito takarar shugabancin ƙasa

  • Wata kungiyar matasan Arewa, Arewa Youth Assembly, ta yi kira ga attajiran Najeriya masu kamfanoni su fito takarar shugaban kasa
  • Matasan sun ce bai dace a bar wa yan siyasa na yanzu ragamar shugabancin ba duba da cewa Najeriya na da hazikan yan kasuwa da masu kamfanoni da suka yi fice a duniya
  • Kungiyar ta ce attajiran sun san yadda aka habbaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi kamar yadda suka yi a kamfanoninsu don haka su ya dace su jagoranci Najeriya

Matasan arewa karkashin kungiyar Arewa Youth Assembly, sun yi kira ga fitattun yan kasuwa a kasar su fito su ceci kasar ta hanyar yin takarar shugabancin kasa a 2023, rahoton The Punch.

A cewarsu, Najeriya na bukatar basira da shugabanci irin na mutane kamar Alhaji Aliko Ɗangote, Femi Otedola, Mrs Ngozi Okonjo Iweala da sauransu, da suka yi nasara a harkokinsu.

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

2023: Matasan arewa sun roƙi Ɗangote da Otedola su fito takarar shugabancin ƙasa
Matasan arewa sun roƙi Ɗangote da Otedola su fito takarar shugabancin ƙasa a 2023. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Matasan na arewa sun ce bai dace a bar batun shugabancin Najeriya a hannun ƴan siyasan zamanin yanzu ba kuma suka yi kira ga yan Najeriya kada su yarda a rude su da kyautan kudi da kayan abinci a 2023.

The Punch ta rahoo matasan na Arewa sun bayyana hakan ne cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Mohammed Ɗanlami, da magatakarda, Desmond Minakaro a ranar Juma'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun ce:

"Ilimi da ƙwarewar da masu kamfanoni ke samu daga kasuwanci yakan sa ya gano yadda gwamnati ke shafan ɓangaren kasuwanci, wanda shine jigon habbakar tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma.
"A kasa kamar Najeriya da ke da hazikan mutane da ake girmamawa a duniya irin su Mrs Ngozi Okonjo Iweala, Mrs Ibukun Awosika, Mr Bode Augusto, Mr Segun Agbaje, Mr Fola Afrika, Alhaji Tunde Folawiyo, Mr Atedo Peterside, Mr Kola Adesina, Alhaji Aliko Ɗangote, Me Femi Otedola, Mr Herbert Wigwe da Mr Aig Imoukhuede, wadanda ke da ilimin kasuwanci, me yasa za a bari wadanda ba su da wannan ilimin su rika shugabantar kasar?

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

"Duk dan kasuwar da zai iya bunkasa kasuwanci da a kasa mai hadari kamar Najeriya tabbas zai iya jan ragamar kasar.
"Najeriya za ta bunkasa idan ya zama shugaba tunda dama shi mai samar da ayyuka ne kuma zai samar da yanayi da kasuwanci za ta bunkasa.
"Muna rokon yan kasuwa da suka yi nasara a ɓangarorin su su shiga takarar shugaban kasa a 2023, ya zama dole su shiga a dama da su. Muna rokon ku zo ku jagoranci ƙasar nan ba wai kasuwancin ku ba kawai. Ku zo ku ceto Najeriya daga shugabanci maras alkibla."

Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, kwatankwacin ƙarfin tattalin arzikin Senegal

A wani rahoton, kun ji cewa, Alhaji Aliko Dangote ya samu karuwar arziki da kimanin Dala biliyan 1.3 (N539,435,000,000.00) a farkon shekara zuwa ranar 21 ga watan Janairu, a cikin wannan lokacin masu hannu jari a kamfanin simintin Dangote sun samu alheri, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

A halin yanzu arzikin sa ya tasanma na Dala biliyan 20.4 a cewar kididigar Biloniyoyi na Bloomberg a ranar Juma'a, hakan na nufin arzikin na dan kasuwan mafi arziki a Afirka ya kai kusan karfin tatttalin arzikin kasar Senegal da Bankin Duniya ta kiyasta ka Dalla biliyan 24.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164