Da Dumi-Dumi: Bamu yadda a yi zaɓen fidda gwani ba, Matasan APC sun barke da zanga-zanga a jihar Ekiti

Da Dumi-Dumi: Bamu yadda a yi zaɓen fidda gwani ba, Matasan APC sun barke da zanga-zanga a jihar Ekiti

  • A yau Alhamis, jam'iyyar APC mai mulki ta shirya gudanar da zaben fidda gwani a jihar Ekiti
  • Sai dai zaben ya zo da matsaloli, yayin da mambobin jam'iyyar suka ɓarke da zanga-zanga a hedkwata domin nuna adawar su
  • Masu zanga-zanga sun zargi cewa gwamnan jihar, Kayode Fayemi. ya shirya maguɗi a zaɓen

Ekiti - Mambobin jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Ekiti sun fara zanga-zangar nuna adawa da zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan jihar.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa APC ta shirya gudanar da zaɓen fitar da gwani ne a yau Alhamis, 27 ga watan Janairu, 2022.

APC a Ekiti
Da Dumi-Dami: Bamu yadda a yi zaɓen fidda gwani ba, Matasan APC sun barke da zanga-zanga a jihar Ekiti Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mambobin waɗan da suka mamaye hedkwatar jam'iyya ta jiha, sun zargi gwamnatin APC dake mulkin jihar da shirya manaƙisa a zaɓen.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai miƙa mulki ga ɗan takarar APC a 2023 Insha Allahu, Garba Shehu ya magantu

Duk da tuni aka fara tantance masu zaɓen a wasu gundumomin jihar, amma mambobin jam'iyya dake zanga-zanga a Sakateriya sun ce ba za su yi zaɓen ba.

"Ba mu yarda da zaɓen ba, ba bu wani zaɓen fidda gwani," Mambobin APC suka cigaba da faɗa a Sakatariya.

Wasu jiga-jigan APC sun bukaci a ɗage zaben

Wannan na zuwa ne bayan mamba a majalisar dattawan Najeriya daga jihar Ekiti, Opeyemi Bamidele, ya bukaci a ɗage zaben fidda gwanin.

Kazalika ɗaya daga cikin masu hankoron tikitin takarar gwamna karkashin APC, ya goyi bayan dakatar da shirin zaben fitar da gwanin a yau Alhamis.

Da safiyar yau ne, mutum bakwai daga cikin yan takara dake neman tikitin APC suƙa bayyana janye wa daga zaɓen baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne bisa zargin shirya magudi da gwamnan jihar, Kayode Fayemi, ya yi.

A wani labarin na daban kuma Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta gamu da cikas, yayin da ɗaruwawan mambobinta suka koma APC a mazaɓar Ovia.

Masu sauya sheƙan sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda ayyukan raya ƙasa da ɗan majalisa mai wakiltar Ovia a tarayya ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262