Ba zai taba zama shugaban kasa ba, Fasto ya yiwa gwamnan wata jiha baki
- Primate Elijah Ayodele ya yi hasashe mara dadi a kan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
- Babban malamin kiristan yace Wike ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba
- Ya kuma gargadi shugabannin jam'iyyar adawar da su yi hankali sannan su gyara abubuwa idan ba haka ba za su sha kaye a babban zaben 2023
Rivers - Babban limamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.
Faston ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa, Osho Oluwatosin, ya saki a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.
Malamin addinin ya kuma yi gargadin cewa Wike zai rusa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) idan shugabannin jam'iyyar adawar ba su gyara abubuwa ba, PM News ta rahoto.
Primate Ayodele ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya kuma zama dole ya yi taka-tsan-tsan don kada ya rusa PDP. Yana iya sa PDP ta sha kaye a zaben 2023 idan ya ci gaba da kawo cikas a jam'iyyar.
"Yakamata kwamitin amintattu na PDP su duba lamarin idan ba haka ba za su fadi."
Gwamnonin PDP za su yake shi sannan EFCC za ta bibiyi gwamnatinsa
Da yake ci gaba da magana kan Wike, Primate Ayodele ya bayyana cewa ya hango gwamnonin PDP suna fada da shi yayin da EFCC kuma za ta bi gwamnatin sa.
Ya ce:
"Na hango gwamnonin PDP suna fada da Nyesom Wike. EFCC ma za ta bibiyi gwamnatinsa."
Ya ci gaba da gargadin Wike da kada ya yi takarar shugaban kasa saboda ba zai taba zama shugaban Najeriya ba.
"Kada Wike ya fara aikin da ba zai iya gamawa ba a PDP. Ba zai zama shugaban kasa ba koda a ce yana da aniyar."
Kan PDP, Ayodele ya kuma gargadi shugabannin da su yi taka-tsan-tsan don kada su rusa jam'iyyar da kansu.
Ya ce wata tawaga ta uku na iya tasowa daga jam’iyyar adawa saboda ayyukan shugabannin.
Faston ya kuma magantu a kan makomar Iyochia Ayu, shugaban PDP na kasa, ya ce za a kwace aikinsa sannan kuma a kore shi daga jam’iyyar, rahoton Daily Post.
2023: Babban faston Najeriya ya bayyana wanda zai gaji Buhari
A gefe guda, mun ji a baya cewa yayin da shekarar 2023 ke kara gabatowa, 'yan Najeriya da dama sun zuba ido domin ganin wanda zai karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari gabannin babban zabe mai zuwa.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, babban malamin na addinin Kirista, ya ambaci wasu manyan yan siyasa da ka iya zama shugaban kasar Najeriya da mataimakinsa a 2023.
Asali: Legit.ng