Ban yi wa Buhari kamfen ba, hotunansa kawai na wallafa, Dele Momodu
- Mawallafin Mujallar Ovation, Mr Dele Momodu ya musanta cewa ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kamfen
- Momodu ya bayyana cewa abin da ya yi kawai shine wallafa hotunan Buhari amma bai tilasta wa kowa ya fita ya zabe shi ba
- Mai neman takarar shugaban kasar a 2023 ya ce ba shi da matsala da halin Buhari amma bai yarda da irin siyasarsa ba
Mr Dele Momodu, mawallafin Mujallar Ovation, ya ce bai taba yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kamfen ba, The Cable ta ruwaito.
Momodu ya bayyana hakan ne a hirarsa da Chude Jideonwo, dan jarida.
Da ya ke magana kan ra'ayinsa game da shugaban kasa, Momodu yace:
"Gaskiya ina son sa don kashin kansa amma bana son siyarsa, sam sam."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai neman takarar shugaban kasar a 2023 ya musanta zargin da ake yi na cewa ya yi wa Buhari kamfen na shugabancin kasa.
"Ni ban tallata muku Buhari ba. Kawai abin da na yi shine wallafa hotuna. Babu yadda wani zai ce, na ce dole sai ka tafi ka zabi Buhari," in ji shi.
"Yan Najeriya sun tsinci kansu a halin da suke ciki a yanzu ne saboda suna gaza raba kansu da wadanda suka dauki siyasa a matsayin sana'a.
"Amma ba zai yi wu Najeriya ta cigaba da wannan haukan ba. Abin da yasa muka gaza samun cigaba shine don muna cikin bacin rai da bakin ciki."
Momodu ya kuma yi magana kan yadda ya zauna cikin fargaba a Landan bayan ya tsere daga gwamnatin soja na Janar Sani Abacha, tsohon shugaban Najeriya.
Gwagwarmayar da na sha don tserewa Abacha
Ya bada labarin yadda fashewar wani bam ya firgita shi da ma'aikatansa a ofishinsu da ke Canary Wharf a Landan.
Ya ce:
"Mun samu ofishi da kujeru na hannu. Sai muka siya giya don mu yi murnar samun ofis duk da cewa ba mu san inda za mu samo kudin biyan printers ba.
"Kawai muka ji boom! Bam ya tashi ginin da ke kusa da mu. Kimanin gine-gine 100 suka tarwatse.
"Muka fara gudu, na fara ihu ina cewa Abacha! Abacha!.
"Ina tunanin Abacha ya gano inda muke ne. Sai muka gudu, muka ga karnukan yan sanda a ko ina, ashe kowa ya fice daga wurin banda mu domin muna can muna shagali.
"Amma mun yi sa'a ginin da muke yana da kariya na bam shi yasa bai rushe ba."
Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare
A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.
Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng