Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

  • Jigon APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Sani Musa
  • Musa na daya daga cikin manyan yan takarar kujerar shugaban jam'iyyar mai mulki na kasa
  • Tinubu ya ba dan majalisar tabbacin cewa jam'iyyar za ta saka masa sakamakon sadaukarwar da ya yi wajen nasararta a 2014 da 2015

Abuja - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Sani Musa (APC Neja).

Ziyarar Tinubu na zuwa ne kwanaki uku bayan Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya lamunce ma kudirinsa na neman takarar shugaban kasa.

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC
Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC Hoto: Nigerian Youth Movement
Asali: Facebook

Sanata Musa na daya daga cikin manyan yan takara da ke neman takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC na kasa a babban taron jam'iyyar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Zamu saka maka bisa abubuwan da ka yiwa jam'iyya, Tinubu ga dan takaran shugaban APC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a yayin ziyarar da jigon na APC ya kai gidansa da ke Maitama a Abuja, Tinubu ya ba Sanata Musa tabbacin cewa dukka sadaukarwar da ya yiwa jam'iyyar ba zai tafi a banza ba.

Tinubu ya ce jam’iyyar za ta ba dan majalisar tukuicin sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar ta a 2014 da 2015, rahoton The Nation.

Tinubu ya ce:

“Sadaukarwar da fitaccen Sanata Mohammed Sani Musa ya yi a shekarar 2014 da 2015 ba zasu tafi a banza ba, shugabancin jam’iyya mai mulki na sane da shi kwarai da gaske. Insha Allahu za a bashi lada."

Magana ta canza: Sanatan APC ya ce yanzu da shi za a nemi takarar Shugaban kasa a 2023

Kara karanta wannan

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

A wani labarin, Punch ta rahoto Orji Uzor Kalu yana cewa a baya ya fadawa irinsu Sanata Anyim Pius Anyim da David Umahi cewa ba zai nemi shugabancin kasa ba.

Amma da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Silverbird Television a ranar Juma’a, 21 ga watan Junairu 2022, Sanatan ya ce ya canza shawara a halin yanzu.

A cewar Orji Uzor Kalu, mutane daga duka bangarorin kasar nan sun same shi, sun kuma roke shi ya fito neman titikin takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng