Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Bayan ya ayyana aniyarsa ta yin takara a zaben shugaban kasa na 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi wasu babatu da ka iya kai sa su baro a kudirinsa na son darewa kujerar shugabancin.

Yawancin furicin da babban jagoran jam’iyyar ta All Progressives Congress (APC) na kasa ya yi kan lamuran da suka addabi kasar ne wanda yan Najeriya ke Allah Allah a magance su.

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023
Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin wadannan kalamai na Tinubu tare da duba illar da za su iya yi masa.

1. Zan shafe rashin tsaro

A ziyarar da ya kai Zamfara domin yiwa gwamnati da mutanen jihar jaje bayan yan bindiga sun farma wasu garuruwa, Bola Tinubu, yayin da yake bayar da tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da lamarin ya ritsa da su, ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta shafe Boko Haram.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Ya ce:

“Za a yi maganin makiyan ilimi, Boko Haram da sauran miyagu ta hanyar jajircewa.
“Muna addu’ar daidaituwar kasa baki daya kuma idan makiyan suka ki daina ta’assar, za mu shafe su...”

Ga wasu yan arewa wadanda suka yanke kauna da gwamnati kan yawan hare-hare da yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke kai masu, wannan jawabin wanda aka yi don sake basu tabbaci na iya harzuka su da yanke kauna domin haka aka saba yi masu alkawari.

2. Katin zabe sun lalace

A jawabinsa ga shugabannin mata da suka kai masa ziyara a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa katin zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta raba sun lalace.

An jiyo yana cewa:

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa a 2021: Yadda hauhawar farashin kayayyaki ya kasance a kowane wata

“Koda basu sanar maku ba a kan lokaci, katin da kuke da shi ya lalace.
“Ku dauki iyalanku daya, iyalanku biyu, ku kwankwasa dukka kofofi sannan ku tabbatar da ganin cewa an yi sabon rijista... Saboda ba lallai ne su sanar maku a kan lokaci ba. Katin zabe da kuke da shi ya lalace. Eh!”

Koda dai Tonubu ya bayar da hakuri daga baya a ranar Talata,18 ga watan Janairu, ta kakakinsa, Tunde Rahman, saboda yin wannan jawabi da ba gaskiya ba, wasu yan Najeriya na iya kallonsa a matsayin wanda baya tabbatar da gaskiyar zance kafin ya yada ta.

3. Zan biya kudin WASSCE din kowani dan Najeriya

A wani bidiyo da The Nation ta sanya ido a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, Tinubu ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa zai biya kudin jarrabawar WASSCE na kowani dalibi idan ya zama shugaban kasa.

Tsawon shekaru da dama, gwamnatin tarayya na ta fafatawa da Kungiyar malaman ASUU lamarin da ke haifar da shiga yajin aiki wanda ke kawo tsaiko ga makarantun jami’a.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Don haka, wannan magana ta Jagaban ba ta ko tabo dimbin matsalolin da ke bangaren ilimi ba, balle a yi maganar samar da mafita ta dindindin.

‘Yan Najeriya da ASUU suna son ganin fannin ilimi ya dawo kan kafarsa, ba wai daukar wasu alkawura da kawai ke nuna tsohon gwamnan Legas a matsayin mai taimakon jama’a ba.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa.

Bello, ya sanar wa masoyansa dake faɗin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng