Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

  • Gwamnan Jihar Borno, Farefesa Babagana Zulum ya ce ba shi da niyyar yin takarar wata kujerar siyasa a zaben shekarar 2023
  • Hakan na zuwa ne yayin da jita-jita ke bazuwa cewa Zulum zai yi takara a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya a 2023
  • Zulum ya bayyana cewa tun farko ma shi bai taba tunanin zai zama gwamnan Jihar Borno ba sai dai ya yi addu'ar Allah ya zaba masa abin da ya fi alheri

FCT, Abuja - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
Ba ni da niyar sake neman wata kujerar siyasa a 2023, Zulum. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Ya ce:

"Muna kara matsowa shekarar 2023 inda za a yi babban zabe, amma a wuri na bai da wani muhimmanci. Ba na fatan neman wata kujera. Ban taba fatan zan zama gwamnan Jihar Borno ba ma kuma bana fatan sake neman wata kujerar da ta fi ta amma a matsayin na na musulmi, ina addu'ar abin da ya fi alheri."

Ya shawarci mutane su rika duba yiwuwar zaben shugabanni na gari a maimakon mayar da hankali kan zaben kansa.

"Ya kamata mu rika duba yiwuwar zaben shugabanni na gari, ko muna so ko bamu so. Ta yaya? wannan babban tambaya ne; ko da a APC ko PDP, ina tunanin ya kamata mu rika duba yadda za mu zabi shugabanni na gari."

Kara karanta wannan

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164