2023: Ya zama tilas PDP ta samar da shugaban ƙasa a zabe mai zuwa, In Ji Fayose
- Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce ya zama dole babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samar da shugaban kasan Najeriya na gaba
- Ya fadi hakan ne a matsayin tabbaci akan cewa lallai jam’iyyar zata lashe zaben shugaban kasa da ke karatowa a shekarar 2023
- Fayose ya yi wannan furucin ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a wani shirin gidan talabijin din Channels na Siyasa a Yau, ranar Laraba
Jihar Ekiti - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ce za ta samar da shugaban kasa mai zuwa, The Punch ta ruwaito.
Ya fadi hakan ne a matsayin tabbaci akan cewa jam’iyyar ta gama shirin lashe zaben 2023 na shugaban kasa.
Fayose ya yi wannan bayanin ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Channels ya yi da shi a wani shiri na Siyasa a Yau, ranar Laraba.
Ya yaba da tsarin shugaban jam’iyyar PDP
Kamar yadda ya ce:
“Ya zama dole PDP ta samar da shugaban kasa mai zuwa. Babu wanda zai sake zaben APC. Gwamnatin ta rasa makama saboda mawuyacin halin da ta jefa jama’a. Mutane a yunwace suke amma kana can kana hada dalar shinkafa maimakon ka tallafa musu da ita.”
Ya yaba wa shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu akan yadda ya ke da tsari cike da natsuwa da sanin ya kamata.
Ya ce shugaban jam’iyyar ya dakatar da duk wasu masu mukami akan zuwa gidan sa don rokon alfarma.
Ya ce yana girmama Tinubu
Yayin da aka bukaci ya yi tsokaci akan shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce yana girmama Tinubu saboda shugaba ne na Yarabawa, amma jam’iyyar sa bata burge shi.
Ya bayyana abinda ya hana shi takarar shugabancin kasa a 2023 inda yace saboda burinsa na tabbatar da hadin kan jam’iyyar a Jihar Ekiti.
Kamar yada ya ce:
“Na yarda da cewa duk wanda ya ke son mulkin Najeriya sai ya fara mulkar jihar sa. Ina aiki tukuru ne don hada kan ‘yan jam’iyyar mu don ta lashe zaben gwamnoni na jihar ko ni na kai dan takarar ko ba ni bane.
“Ko da tsohon gwamnan jihar, Segun Oni ya lashe zaben fitar da gwani, zan mara masa baya.”
2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.
Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng