Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023
- Matashi mai jini a jika, ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa zaben 2023 mai zuwa
- Matashin da ga Shehu Dahiru Bauchi, ya bayyana cewa, ya cancanci wannan kujera ta Buhari a zabe mai zuwa
- Wannan shi ne karo na uku da matasa suka fito suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa
Bauchi - Nazir Tahir, da ga Shehu Dahiru Bauchi ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa nan kusa.
Ya bayyana kudurin nasa ne cikin wani bidiyo da ya yada, inda ya yi bayanin abubuwan da suka ja hankalinsa zuwa tsayawa tsakarar.
A kalaman Nazir, ya ce kamata ya yi dattawa su ba masu jini a jika damar mulkar kasar nan, inda yace an ga kamun ludayinsu amma hakan bai kaw sauyi ba.
Ya ce, an shaida mulkin PDP da APC, amma duk babu wanda 'yan Najeriya suka mora, kasancewar ba matasa bane ke rike da madafukn iko.
Dan na Shehu Dahiru Bauchi ya fito ne a jam'iyyar APGA, jam'iyyar da a kwanan nan ta lashe zaben gwamna a jihar Anmabra.
A shafinsa na Facebook, Nazir tuni ya fara yada hotuna da wakokin neman takararsa, inda magoya da dama suka bayyana goyon baya ga wannan manufa.
Duban da wakilinmu ya yi zuwa shafin nasa, ya ga wata wata waka da aka rerewa Nazir, wacce ke bayyana halaye da manufar dan takarar.
Yana daga cikin masu kananan shekaru da suke neman takara
Duba da bayanansa na shafin Facebook, an haifi Nazir ne a 1985, wanda akalla yanzu ya kai shekaru 37 kenan.
Baya ga Nazir, an samu wasu matasa da suka nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben na 2023 mai zuwa.
A baya kadan, Khadijah Okunnu-Lamidi, ‘yar kasuwa kuma mai fafutukar ci gaban matasa ta bayyana sha’awarta na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Legit.ng ta tattaro cewa Okunnu-Lamidi ta bayyana sha’awarta ta maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a shekarar 2023 a wani taron manema labarai da aka gudanar a filin shakatawa na Freedom da ke Legas.
Matashiyar 'yar shekaru 38 a cikin wata sanarwa da ta yada a shafinta na yakin neman zabe ta bayyana cewa burinta shi ne kawar da mugunyar fatara da kebe al'umma tare da maido da fatan samun makoma mai kyau ga 'yan Najeriya.
Okunnu-Lamidi ta kuma bayyana cewa dalilin da ya sa ta nemi tsayawa takarar kujerar mafi girma a kasar ya samo asali ne daga burinta na ganin Najeriya ta yi wa al’ummarta ayyuka mabambanta masu amfani.
Yayin da ta ke bayyana rashin jin dadinta ga yadda Najeriya ta rasa wasu muhimman matakai na ci gaba, ‘yar kasuwar ta bayyana cewa burinta shi ne maido da martabar kasar ta hanyar shugabanci nagari.
A bangare guda, wani matashi dan kimanin shekara 35 dan asalin jihar Kano dake Arewa maso gabas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Matashin mai suna Aminu Sa'idu yace ya shirya tsaf domin tsayawa takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Aminu Sa'idu ya fadawa jaridar Daily Trust cewa zai tsaya takarar ne saboda dokar kasa da tace 'Ban yi kankanta da tsayawa takara ba'.
Asali: Legit.ng