2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria zai tsaya takarar shugaban ƙasa a APC

2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria zai tsaya takarar shugaban ƙasa a APC

- Wani matashi ɗan kimanin shekaru 35 daga jihar Kano dake Arewa maso yammacin kasar nan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APC a babban zaɓe mai zuwa 2023

- Matashin yace dokar da shugaba Buhari ya kafa ta 'Ban yi ƙanƙanta ba da yin takara' ita ce ta bashi ƙarfin guiwar fitowa a dama dashi

- Matashin mai suna Aminu Sa'idu ya kammala karatun digirinsa na farko a jami'ar Bayero dake Jihar Kano.

Wani matashi ɗan kimanin shekara 35 ɗan asalin jihar Kano dake Arewa maso gabas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa.

KARANTA ANAN: Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa

Matashin mai suna Aminu Sa'idu yace ya shirya tsaf domin tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.

Aminu Sa'idu ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa zai tsaya takarar ne saboda dokar ƙasa da tace 'Ban yi ƙanƙanta da tsayawa takara ba'.

A cewar Aminu wannan dokar na da tasiri wajen karawa matasa yan siyasa karmashin karfin gwuiwa su fito a dama dasu a kowanne matakin zabe na ƙasar nan.

2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC
2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC Hoto: @OfficialAPCKD
Asali: Twitter

Ɗan takarar, wanda ya kammala digirinsa na farko a fannin tattali a jami'ar Bayero dake Kano (BUK) yana fatan 'yan Najeriya da kuma 'yayan jam'iyyarsa ta APC zasu mara mishi baya.

KARANTA ANAN: 'Yan Bindiga sun hallaka wani Sufeton 'yan sanda, Sun babbaka motarsu a Delta

Aminu Sa'idu yace:

"Muna bukatar mu bayyana a aikace cewa 'Bamu yi ƙanƙanta da takara ba' saboda mu mutane ne wanda damuwar mu shine Najeriya ta cigaba."

"Ina ganin matuƙar shugabannin mu na baya sun yi aiki mai kyau tun suna da ƙananun shekaru kamar; Tafawa Balewa, Amadu Bello Sardauna, Murtala Muhammad da kuma Abubakar rimi zasu kafa babban tarihi a zamanin su na mulki a matsayinsu na matasan shuwagabanni,"

"Muma matasan yanzun zamu iya amfani da wannan damar mu kafa wani sabon tarihi a ƙasar nan," Inji Aminu.

A wani labarin kuma Kwamishina ya fara aiki a karkashin bishiya saboda babu ofishin da zai shiga a Taraba

Abin mamakin shi ne Mista Yakubu ya fara aikinsa ne a karkashin bishiya bayan sakadaren din-din-din na ma’aikatar jihar ya mika masa ragamar aiki.

Jethro Yakubu zai rika aiki a karkashin bishiya ne kafin ya samu wurin zama.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262