Da duminsa: Za mu sake gabatar da sabon kudirin gyaran dokokin zabe, Gbajabiamila
- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce za su sake gabatar da sabon kudirin gyaran dokokin zabe a gaban majalisar
- A cewar Femi Gbajabiamila, za a gabatar da sabbin kudirin zaben a ranar Laraba a zauren majalisar
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da bukatar 'yan majalisar na kallafa salon zaben fidda gwani na kato bayan kato
FCT, Abuja - Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya ce sabon kudirin gyaran dokokin zaben za a gabatar da shi a zauren majalisa nan da ranar Laraba.
Gbajabiamila ya sanar da hakan ne a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, ya yi jawabin ga abokan aikinsa wadanda suka dawo hutun wannan shekarar, TheCable ta ruwaito.
TheCable ta ruwaito yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki saka hannu kan sabon kudirin zaben inda ya kafa hujja da rashin amfanin salon zaben fitar da gwani na kato bayan kato.
Shugaban kasan ya ce, wannan salon zaben fidda gwanin idan aka ce dole ne ga jam'iyyun siyasa "ya karya dokokin damokaradiyya".
“Majalisar za ta sake gabatar da gyararrun dokokin zabe gobe kuma za mu yi hanzarin aiki a kai tare da mika ta gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari domin amincewa," kakakin majalisar yace.
Dalilai 14 kwarara da suka sa Buhari ya yi watsi da Kudirin gyaran dokar zaɓe
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya yi bayanin dalilan da suka sa ya ki amince da kudirin gyaran dokar zaben kasar nan wanda ya mayar wa majalisar tarayya.
An karanta wasikar shugaban kasan na kin amincewa da bukatar a dukkan zaurukan majalisar kasar nan, The Nation ta ruwaito.
Ga wasu daga cikin dalilai 14 da suka sa shugaban kasan ya ki sanya hannu kan kudirin domin ya zama doke.
1. Salon zaben fidda gwani na kato bayan kato ya na da matsala kan kudi, shari'a, tattalin arziki da tsaro wanda kasar nan ba za ta iya tunkara yanzu ba.
2. Idan kudirin ya zama doka, zai iya taba damar 'yan kasa wurin taka rawa a gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.
3. Babu shakka yin zaben fitar da gwani na salon kato bayan kawo a gundumomi 8,809 na kasar nan zai matukar cin kudin jam'iyyun siyasa.
Asali: Legit.ng