Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari

Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya magantu a kan dan takarar da ya kamata ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa yakamata shugaban Najeriya na gaba ya zamo mutum da ya fi shi karancin shekaru, mai jini a jika
  • IBB ya kuma ce akwai bukatar magajin Buhari ya zamo mai iya zance wanda ke da wani a dukka yankunan kasar

Niger - Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya jadadda matsayarsa kan cewa ba zai marawa tsoho baya ba a zaben shugaban kasa na 2023.

A wata hira da yayi da jaridar Daily Trust a baya-bayan nan, IBB ya jero wasu sharudda da suka zama dole duk mai neman kujerar shugaban kasa a 2023 ya cike.

Kara karanta wannan

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari, babu Tinubu da Atiku ciki
Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari, babu Tinubu da Atiku ciki Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ba zai taba marawa wanda ya haura shekaru 60 baya don zama shugaban kasa ba, rahoton PM News.

Ya ce dole ne shugaban kasa na gaba ya fi shi karancin shekaru sannan ya zama mara kabilanci wanda ya san wani daga kowani yanki na kasar.

Baya ga shekaru, IBB ya bayyana cewa dole ne shugaban kasa na gaba ya zamo mai iya zance sosai.

Ya kuma bayyana cewa dole ne shugaban Najeriya na gaba ya dunga yi wa mutane jawabi kan duk wani abu da ya shafi kasar.

Ya ce:

"Ba zancen wa nake da shi a zuciya bane sai dai wanda ya dace; duk wani mutum da ya cike wadannan, toh shine mutumin da ya dace idan dai shi dan Najeriya ne; dan siyasa ne, ba tsoho kamana ba; ya san kan kasar sosai, mai iya zance, ya iya magana sosai.

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

“Ya kamata ya iya zance saboda ya kamata shugaban kasa ya iya shiga cikin jama’a yana tattaunawa da su kan batutuwan da suka shafi Najeriya; ba koyaushe ba amma mafi yawan lokuta.
"Dole ya kasance da wani da ya sani a duka yankunan kasar. Ba dogon tsari bane.
“Kana iya takaita shi a jihohi, kana iya takaita shi ga kananan hukumomi ko ga unguwanni idan za ka iya amma ya zama wani wanda da zarar ka ji sunan, zai kasance mutum da za ka ce, eh, na taba jin wannan sunan a baya ko dai a cikin kasar ko a kan sana'arsa; idan shi likita ne, ko dan jarida ko ma wanene, a dukka bangarori, mun taba jin sunan a baya; to, zan yi kokari don samun karin bayani a kan shi."

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Mun kawo a baya cewa tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana yadda za a iya raba kasar da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari yace yayin da Tinubu ya ce ba abin da zai hana shi zama shugaba a 2023

A wata hira da Trust TV, tsohon dan siyasar ya bayyana cewa ya yi ritaya daga siyasa amma har yanzu yana da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a bangaren siyasa.

Ya ce:

"Eh nayi ritaya daga siyasa; bana siyasa amma har yanzu ina da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a siyasar saboda wannan ce kasata, bani da wata kasa, dole na samu ra'ayi a abun da ke wakana."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng