Masu jini a jika: 'Yar shekara 38 ta ce ba wanda ya dace ya gaji Buhari sai ita a 2023

Masu jini a jika: 'Yar shekara 38 ta ce ba wanda ya dace ya gaji Buhari sai ita a 2023

Khadijah Okunnu-Lamidi ta zama mace ta farko da ta bayyana sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Mtashiyar mai shekaru 38 ta bayyana sha'awar maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin kasar nan

A cewar Khadijah, abin da ya sa ta yanke sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa ba dan komai bane sai don sha'awar gyara Najeriya

Legas - Khadijah Okunnu-Lamidi, ‘yar kasuwa kuma mai fafutukar ci gaban matasa ta bayyana sha’awarta na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Legit.ng ta tattaro cewa Okunnu-Lamidi ta bayyana sha’awarta ta maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a shekarar 2023 a wani taron manema labarai da aka gudanar a filin shakatawa na Freedom da ke Legas.

Mtashiya mai burin zama shugaban kasa a Najeriya
Masu jini a jika: 'Yar shekara 38 ta ce ba wanda ya dace ya gaji Buhari sai ita a 2023 | Hoto: @Kol_nigeria
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Mtashiyar 'yar shekaru 38 a cikin wata sanarwa da ta yada a shafinta na yakin neman zabe ta bayyana cewa burinta shi ne kawar da mugunyar fatara da kebe al'umma tare da maido da fatan samun makoma mai kyau ga 'yan Najeriya.

Okunnu-Lamidi ta kuma bayyana cewa dalilin da ya sa ta nemi tsayawa takarar kujerar mafi girma a kasar ya samo asali ne daga burinta na ganin Najeriya ta yi wa al’ummarta ayyuka mabambanta masu amfani.

Yayin da ta ke bayyana rashin jin dadinta ga yadda Najeriya ta rasa wasu muhimman matakai na ci gaba, ‘yar kasuwar ta bayyana cewa burinta shi ne maido da martabar kasar ta hanyar shugabanci nagari.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Okunnu-Lamidi

Okunnu-Lamidi wacce har yanzu bata shiga wata jam’iyya ba ta yi digiri na farko a fannin Gudanar da Kasuwanci daga Jami’ar Bolton da digiri na biyu a fannin Strategic Project Management daga Jami’ar Heriot-Watt.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Ita dai diya ce ga Lateef Femi Okunnu (SAN), tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje na tarayya kuma dattijon kasa yayin da mahaifiyarta, Arinola Omololu, ita kuwa ‘yar kasuwa ce.

Hakazalika tana auren Adeshola Lamidi, kwararre kan harkokin kudi. Ma'auratan suna da 'ya'ya.

A bangare guda, wani matashi dan kimanin shekara 35 dan asalin jihar Kano dake Arewa maso gabas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Matashin mai suna Aminu Sa'idu yace ya shirya tsaf domin tsayawa takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Aminu Sa'idu ya fadawa jaridar Daily Trust cewa zai tsaya takarar ne saboda dokar kasa da tace 'Ban yi kankanta da tsayawa takara ba'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.