2023: Wani na hannun daman saraki ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

2023: Wani na hannun daman saraki ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

  • Hon Mathew Okedare, na hannun daman Bukola Saraki ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Okedare wanda ya kuma kasance tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara ya ce ya sauya shekar ne saboda da nasarorin da gwamnan jihar ya samu ta bangaren ci gaba
  • Sai dai ya ce baya nufin tsohon shugaban majalisar dattawan da sharri kawai dai ra'ayinsa na siyasa ne ya sauya

Kwara - Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon Mathew Okedare, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Okedare, tsohon dan kashenin jam’iyyar kuma mai biyayya ga tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya hade da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance, rahoton Daily Trust.

2023: Wani na hannun daman saraki ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
2023: Wani na hannun daman saraki ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sauya shekar Okedare zuwa APC na zuwa ne yan watanni kadan bayan wani dan kashenin Saraki, Tunji Buhari, ya bar jam’iyyar adawar kasar zuwa mai mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon jama'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

A wata hira da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, dan siyasar ya alakanta hukuncinsa da kokarin gwamna mai ci na inganta jihar da al’umman ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okedare ya ce:

“Eh, Ina iya tabbatar maku da cewa da gaske ne na koma jam’iyyar APC. Na gana da gwamnan don sanar da batun sauya shekana a hukumance.
“A matsayina na mutum mai son ci gaba, ya zama dole na hade da shi saboda kokarinsa na kawo ci gaba a fadin kananan hukumomi 16.”

Kan dangantakarsa da Saraki, tsohon kakakin majalisar ya ce baya da wani mugun nufi a kan tsohon shugaban majalisar dattawan.

Ya ce:

“Siyasa duk ra’ayi ce. Saraki ya fito dani kuma ya kasance daya daga cikin wadanda suka taimaka mani. Sauya shekana bai da wani nasaba da Saraki wanda zan ci gaba da godemawa kan rawar ganin da ya taka a cigaban siyasana, kawai dai ra’ayina ne ya canja.”

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

A wani labarin, akalla mutane hudu ciki harda wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne aka kaiwa farmaki da ruwan acid a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da harin ga yan jarida a ranar Talata, 11 ga Janairu, a Yola, ya ce an kai rahoton harin ga ofishin yan sandan Jimeta.

Fawas Mohammed ne ya shigar da kara a ranar 6 ga watan Janairu sannan aka fara bincike kan lamarin, Sahara Reporters ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng