Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wani abin da zai hana shi zama shugaban kasar Najeriya na gaba a 2023
- Shugaban jam’iyyar APC na kasa wanda ya bayyana kansa a matsayin gogagge ya ce yana da ‘yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
- Tinubu ya ce a matsayinsa na mai martaba abin da zai hana shi zama sarki (shugaban kasa) shi ne idan ya kashe mutum
Abuja - Yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.
Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.
A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Babu wani abu da zai hana mai nada sarki zama sarki sai dai idan yayi kisan kai."
Tinubu ya gana da Buhari
A tun farko, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jigon APC ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a gidan gwamnatin tarayya, jim kaɗan bayan ganawa da Buhari ranar Litinin.
A cewarsa:
"Na sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kudirina, amma ban fada wa yan Najeriya ba, har yanzun ina shawari ne."
Duk da tun baya akwai alamun yana sha'awar kujera lamba Daya a Najeriya, Bola Tinubu, ya kauce wa yin kalaman da zasu nuna kudirinsa kai tsaye, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A wani labari, an yi hira da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.
A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.
A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.
Asali: Legit.ng