Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa

Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa

  • Jigon jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya bukaci Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya bar jam'iyyar APC mai mulki
  • Sowunmi ya bayyana cewa babbar jam'iyyar adawar za ta kai shi matakin shugaban kasa koda ba a yanzu ba
  • Ya ce idan har Bello ya ci gaba da kasancewa a jam'iyyar mai mulki, toh ba za su taba kallonsa a matsayin wanda ya cancanci darewa kujerar Buhari ba kasancewarsa matashi

Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Segun Sowunmi, ya bukaci Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Sowunmi, wanda ya kasance kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP a 2019, ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello zai lallasa Atiku idan suka yi takarar zaben shugaban kasa tare a 2023 – Fani-Kayode

Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa
Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa Hoto: The Sun
Asali: UGC

Yayinda yake amsa tambaya kan wanda zai marawa baya domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, baya ga dan babbar jam'iyyar adawar Sowunmi ya ce:

"Idan an ce da zabi wani daga APC... Ina ganin Yahaya Bello zan kalla.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dalili? Shi (Bello) matashi ne, ya cike rukuninka. Ya kasance gwamna. Ina kallon irin abubuwan da yake yi, na karanta irin mutanen da ke goyon bayansa, amma na san cewa yana cikin jam’iyyar da ba za su taba kallonsa ba.
"Don haka watakila kawai zan fada ma abokina Yahaya, ka zo PDP, koda baka samu shugaban kasa ba a yanzu, za mu mayar da kai shugaban kasa wata rana a jam'iyyarmu. Amma idan ka tsaya a waccen jam'iyyar, ban yarda da su ba. Ba sa son matasa... kawai abun da suke sha'awa shi ne kokarin cike gibinsu akan abin da suke kira a matsayin Najeriya a yanzu."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

Rahoton ya kuma kawo cewa duk da matsayinsa a kan Gwamna Bello, Sowunmi ya yarda cewar Atiku ne dan takara daya tilo da ya cancanci a zaba a zaben 2023.

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasar yana da abun da ake bukata ga shugaban kasa na gaba, kamar shekaru da lafiya, addini, al'ada da kuma yanki, kyawawan dabi'a, kuma mutumin da ka iya gyara kasar.

Ya ce:

"Ina fada a kodayaushe, idan ana magana kan Atiku Abubakar, batun ba wai daga inda ya fito bane; batun shine game da irin ra'ayoyin da ya ke da shi tsawon shekaru."

Yahaya Bello zai lallasa Atiku idan suka yi takarar zaben shugaban kasa tare a 2023 – Fani-Kayode

A gefe guda, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zai kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar idan suka yi takarar kujerar shugaban kasa tare a 2023.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, ana ta rade-radi kan wadanda za su zamo yan takarar manyan jam'iyyun kasar guda biyu na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

A wata da Channels TV a ranar Juma'a, Fani-Kayode ya ce ya yarda Bello zai zama 'nagartaccen shugaban kasa', inda ya kara da cewar gwamnan na Kogi zai tafi da matasan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng