Yahaya Bello zai lallasa Atiku idan suka yi takarar zaben shugaban kasa tare a 2023 – Fani-Kayode
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya yi hasashen cewa Gwamna Yahaya Bello zai kayar da Atiku Abubakar idan suka tsaya takarar shugaban kasa a 2023
- Fani-Kayode ya ce Yahaya Bello zai zama nagartaccen shugaba kuma matashi na matasa
- Ya ce mutum biyu da za su iya ba APC ciwon kai a zaben shugaban kasa mai zuwa sune Gwamna Bala Mohammed da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zai kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar idan suka yi takarar kujerar shugaban kasa tare a 2023.
Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, ana ta rade-radi kan wadanda za su zamo yan takarar manyan jam'iyyun kasar guda biyu na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).
A wata da Channels TV a ranar Juma'a, Fani-Kayode ya ce ya yarda Bello zai zama 'nagartaccen shugaban kasa', inda ya kara da cewar gwamnan na Kogi zai tafi da matasan Najeriya, The Cable ta rahoto.
Kayode ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na yi amanna da Yahaya Bello. Na yarda cewa zai zamo nagartaccen shugaban kasa. Na yarda zai. Na yi imani zai tafi da miliyoyin matasa a kasar nan kuma wannan yanayi za mu mika mulki ga matashi. Wannan ra'ayina ne kawai."
Da aka tambaye shi ko Bello (a matsayin dan takarar APC) zai iya kayar da Atiku na PDP a zaben, tsohon ministan ya ce gwamnan na Kogi zai kayar da tsohon mataimakin shugaban kasar, ruwayar Daily Post.
Ya ce:
"Me zai hana? Shi (Bello) zai kayar da Atiku hankali kwance."
Tsohon ministan ya kara da cewar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da takwaransa na Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi daga PDP ne kadai za su iya ba APC ciwon kai a zaben shugaban kasa na 2023.
Fani-Kayode ya bukaci Mohammed da ya dawo APC don yin takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki idan PDP ta ki bashi dama.
Ya kara da cewa:
"Akwai mutane biyu da za su iya ba APC ciwon kai a PDP, mutum biyu ne kawai. Na farko shine Bala Mohammed, wanda nake ganin mutuncinsa sosai.
"Amma ina shakku idan za su bashi tikiti za ma su tabbatar da ganin cewa bai samu tikitin ba ko kuma ya dawo APC ya gwada sa'arsa.
"Sannan Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu wanda baya cikin jerin mutanen (jerin wadanda ka iya zama shugaban kasa da Channels TV ta tattara) kuma yana daya daga cikin mutane masu karfi. Su ne mutane biyu da za su bayar da ciwon kai.
"Babu kuma wani a jerin nan, musamman Atiku Abubakar, da zai iya tsayawa da wani dan APC, musamman Yahaya Bello, Fashola ko Fayemi. Wannan ra'ayina ne kawai, kuma ina da dalilina na fadin haka."
Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu
A wani labari na daban, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu, ya ce yan Najeriya ne suka matsawa Shugaba Muhammadu Buhari don ya tsaya takarar shugaban kasa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Shehu na martani ne ga wasu kalamai da shugaban kasar ya yi kan shirya-shiryensa kan zaben shugaban kasa na 2023.
Buhari, a wata hira da aka watsa a tashar NTA a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, ya ce ya yi iya bakin kokarinsa ga Najeriya, inda yace yana duba ga lokacin da zai huta bayan barin kujerar mulki a 2023.
Asali: Legit.ng