Gazawa: Buhari ya bayyana abin da yake ji a ransa idan aka ambaci PDP a kusa dashi
- Shugaba Buhari ya danganta jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya da alamar gazawa duk da irin kokawa da take da mulkinsa
- Shugaban na Najeriya a wata hira da yayi da gidan Talabijin yace " gazawa" na zuwa a ransa a duk lokacin da aka ambaci jam'iyyar PDP
- Jam’iyyar APC mai mulki ta kawo karshen mulkin PDP a lokacin da shugaba Buhari ya kayar da Jonathan a zaben 2015
Ado Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gazawa ce ke zuwa a zuciyarsa a duk lokacin da aka ambaci jam’iyyar PDP.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a daren Laraba, 5 ga watan Janairu, wacce Legit.ng ta bibiya.
Da aka tambaye shi kan abin da ke zuwa a ransa a lokacin da aka ambaci jam’iyyar adawa, Shugaba Buhari ya amsa da cewa, “gazawa”.
An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su
Jam’iyyar PDP ta mulki Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2015 lokacin da jam’iyyar APCta karbi mulki bayan shugaba Buhari ya doke tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babban zaben 2015.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun hawansa karagar mulki, shugaban ya sha kokawa kan yadda jam’iyyar PDP ta gawa wajen ciyar da Najeriya gaba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki.
Baya ga ambatan batun PDP, shugaban ya yi maganganu da dama a tattaunawar, inda ya tabo batutuwan tsaro, tattalin arziki da kuma ci gaban kasa a dunkule.
Shugaba Buhari ya yi magana game da dan takarar da zai so ya gaje shi a karagar mulki
A cikin hirar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai bada takamaimen amsa ba a yayin da aka tambaye shi game da wanda yake so ya zama magajinsa.
Da aka yi hira da Mai grima Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba, 2021 an bijiro masa da maganar wanda yake so ya karbi mulki a 2023.
Legit.ng Hausa ta bibiya wannan hira inda shugaban kasar ya nuna bai da wani ‘dan takara da yake da shi a rai, wanda zai so ya mikawa ragamar mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng