Ba matsala bane musulmi da musulmi su gaji Buhari da Osinbajo, inji kungiyar magoya bayan Tinubu
- Kungiyar magoya bayan Tinubu ta yi magana game da tsarin bai wa musulmi da musulmi tikitin takarar shugaban kasa gabannin zaben 2023
- Shugaban kungiyar, Abdulmumin Jibrin ya ce ba matsala bane don an baiwa musulmi da musulmi tikitin takarar kujerar
- Ya ce abu mafi muhimmanci shine nagartar wanda zai jagoranci kasar ba wai mika shi ga musulmi ko kirista ba
Abuja - Darakta Janar na kungiyar goyon bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya ce ba matsala bane don Musulmi da Musulmi sun samu tikitin takara yayin da jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki a zaben 2023.
Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai wanda ya jagoranci kamfen din Femi Gbajabiamila don ya zama shugaban majalisar wakilai ta 9, ya ce ‘yan Najeriya sun fi damuwa da nagartar mutanen da za su dare mukaman gwamnati.
Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na Channels TV wanda jaridar Punch ta sa ido.
Jibrin ya ce akwai dubban kungiyoyin goyon bayan Tinubu a fadin kasar, inda ya kara da cewa aikin TSG da yake jagoranta shine kula da sauran kungiyoyin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka tambaye shi ko da gaske ne tsohon gwamnan na jihar Legas zai yi takarar shugaban kasa, tsohon dan majalisar ya ce:
“Eh zai yi takara. Shakka babu, zai yi takarar kujerar… don shugabantar kasa a 2023. Ku kai banki, zai yi takara. Shakka babu. Mun tattauna da shi sosai. Abubuwa da yawa na faruwa a bayan fage.
“Wasu lokutan, nakan yi dariya idan na ga mutane suna cewa ‘Shin zai yi takara ko ba zai yi takara ba?’ Abin da ya rage kawai shine lokacin da zai bayyana aniyarsa, don kawai ya sanar da jama’a cewa, ‘Eh, zan yi takara.’ Amma batun tsayawa takarar Bola Tinubu, aikin gama ya gama. Zai tsaya takarar zaben, zan iya tabbatar muku da haka. Insha Allahu zai kasance a takardar zabe.”
Da yake magana kan batun mika shugabancin kasa ga wani yanki da kuma ko Arewa ta gamsu cewa kujerar ya koma Kudu bayan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Jibrin ya ce idan jam’iyyar APC na so tayi adalci, toh ya kamata mulki ya koma Kudu.
Shugaban na TSG, ya bayyana cewa ’yan takara kan fito daga wasu shiyyoyin a zabukan da suka gabata suna adawa da tsarin karba-karba, yana mai jaddada cewa mutane na da ’yancin tsayawa takara ba tare da la’akari da shiyya-shiyya ba.
Da aka tambaye shi game da makomar yankin kudu maso gabas , ya ce da zarar an mika madafun iko zuwa Kudu, shiyyoyin siyasar yankin suna da damar neman mulki, rahoton PM News.
Da yake amsa tambaya kan tsarin kabilanci da addini idan Tinubu wanda ya kasance Musulmi ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar APC, Jibrin ya ce:
“Na yarda kuma na fahimci cewa kasarmu tana da taka-tsantsan idan ana maganar siyasa, batun kabilanci da addini. Yana da matukar tsanani. Babu wanda zai iya yin biris da wannan.
“Amma idan akan kaina da kuma duba ya yanayin kasar, zan iya tabbatar maku da cewa idan ka ba mutane zabi na mutumin da zai zo sannan ya inganta abubuwan da ke kasa, sannan ya bunkasa tattalin arziki da habbaka kowani bangare da yankin kasar, mutane za su so ganin ci gaba ne kawai. A gareni, wannan ba wani abu bane.
“Idan ka kawo shugabancin Kirista da Kirista ko Musulmi da Musulmi, a ganina, wannan ba wani abun damuwa bane. Hatta a tsakanin jam’iyyar da TSG, mun tattauna kan haka.”
Ya kuma bayyana cewa Tinubu mutum ne mara kabilanci. Ya kuma ce jigon na APC zai yanke hukunci mai kyau wajen zabar abokin takara.
Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade - CAN
A gefe guda, kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ta yi gargadi cewa ba za ta amince a bar musulmai biyu su tsaya a tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba.
CAN tace idan har musulmi da musulmi suka tsaya a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a zaben 2023, kasar nan za ta iya rugujewa.
Jaridar Punch ta rahoto kungiyar ta CAN ta na wannan bayani ne a matsayin martani ga Abdulmumin Jibrin wanda yake da irin wannan ra’ayin.
Asali: Legit.ng