Ba wani Next Level: PDP ta fusata da yadda APC ke zawarcin Jonathan

Ba wani Next Level: PDP ta fusata da yadda APC ke zawarcin Jonathan

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana fushinta ga yadda jam'iyyar APC ke kokarin zawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan
  • Ta ce babu wata tattaunawa tsakanin Goodluck Jonathan da kowane tsagi na jam'iyyar APC domin shiga jam'iyyar
  • Hakazalika, ta bayyana karara cewa, jam'iyyar APC tana yaudarar 'yan Najeriya ne da sunan wani abu wai shi next level

Abuja - Jam’iyyar PDP ta musanta ikirarin cewa jam’iyyar APC na tattaunawa da Goodluck Ebele Jonathan domin kawo tsohon shugaban kasar cikin ta.

Da yake mayar da martani kan rahotannin a ranar Talata, 4 ga watan Janairu, kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce batutuwan ba gaskiya bane, inji rahoton Vanguard.

Ologunagba ya ce jam’iyyar da ke mulki tana ta yada cewa Dr. Jonathan zai shiga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

Jam'iyyar PDP kan batun komawar Jonathan APC
Ba wani Next Level: PDP ta fusata da yadda APC ke zawarcin Jonathan | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Ya yi nuni da cewa, jam’iyyar PDP tana kokari matuka wajen hada jiga-jigan jam’iyyar ciki har da Jonathan, wadanda za su ceto Najeriya daga hannun APC.

A kalamansa:

“Ba ma so mu shiga harkar jam’iyyar da ta nutse wacce ke ci gaba da yaudarar ‘yan Najeriya a koda yaushe.
“A wannan karon, suna ta yada batutuwa cewa mai yiwuwa Dakta Jonathan zai hade tare da su.
“Abin da zan iya cewa shi ne shugabancin kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Dr. Iyorchia Ayu na tuntubar ‘ya’yan jam’iyyar ciki har da tsohon shugaban kasa da su hada kai da ita don taimakawa wajen sake gina Najeriya da ceto ta.
“APC wata mota ce ta musamman da aka kirkira domin ta yi karo da Najeriya a kan wata tafiya marar amfani da ake kira next level. Amma muna kira ga ’yan Najeriya da su hada kai da jam’iyyar PDP domin su taimaka wajen ganin mun dawo da al’umma kan turba baki daya.

Kara karanta wannan

Shugabanci ba na mashiririta da zaman kashe wando bane, APC ta yi wa Shehu Sani martani

"Na fadi cewa ba mu da masaniyar mai girma tsohon shugaban kasarmu sananne a duniya, Dokta Jonathan ya shiga kowace irin tattaunawa da jam'iyyar APC a yunkurin hadewa da su."

A wani lokaci baya, Jonathan da kansa ya yi watsi da jita-jitan zai koma APC, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Ana jita-jitar Jonathan zai koma APC, sai ga PDP ta nemi ganawa dashi kan wani batu

A baya kunji cewa, makwannin da suka gabata an samu rahotannin da ke cewa jam'iyyar APC na zawarcin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonatha, amma PDP ta fito ta yi bayanin gaskiyar lamari.

Wani rahoton The Guardian ya ce, Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar PDP, ya lissafa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, a cikin shugabannin jam’iyyar da za su tuntuba kafin babban taron da za a yi ranar 30 zuwa 31 ga Oktoba.

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, wanda mataimakinsa, Haruna Manu, ya wakilce shi a taron kaddamar da kwamitin, shi ya ba da wannan bayanin, a Abuja ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya fara lale maraba da dawowar tsohon Gwamna Kwankwaso Jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.