Kwara: PDP ta kori mambobinta su 4 sannan ta dakatar da wasu 5 saboda sabawa jam’iyyar
- Jam'iyyar PDP reshen unguwar Adewole da ke karamar hukumar Ilorin West na jihar Kwara ta dauki mataki a kan wasu mambobinta
- Shugaban jam'iyyar yankin ya kori mambobin jam’iyyar hudu sannan ya dakatar da wasu biyar kan zargin yin abubuwan da suka sabawa jam’iyya
- Wadanda aka hukunta sun tabbatar da hakan inda suka ce za su hadu domin sanin mataki na gaba da za su dauka
Kwara - Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a unguwar Adewole da ke karamar hukumar Ilorin West na jihar Kwara ya kori mambobin jam’iyyar hudu sannan ya dakatar da wasu biyar kan zargin yin abubuwan da suka sabawa jam’iyya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 27 ga watan Disamba da kuma sa hannun shugaba da sakaren unguwar, Alhaji Abdulkadir Issa da Alhaji Saad Agbabiaka.
A cewar wasikar, an kori Nureni Omoyooba, Yakubu Agodi, Alao Hakeem da Tunde Muhibudeen yayinda aka dakatar da Misbau Agodi, Tunde Odo, Tunde Khalifa, Alagbon Fatimoh da Moshood Elere daga jam’iyyar.
Taken wasikar shine: “Amincewa da dakatarwa da kuma korar fusatattun mambobi.”
Wani bangare na wasikar ya ce:
“An samu mambobi tara da aka bincika a matakin unguwarsu da laifin sabawa jam’iyya musamman a gidajen radiyo sannan kuma sun nuna rashin da’a ga mahukuntan jam’iyyar.
“An bincikesu bisa adalci kuma an same su da laifin cin amanar jam’iyya wanda ya bayar da damar hukuntasu kamar yadda yake a kundin tsarin jam’iyyar.”
Nigerian Tribune ta rahoto cewa an kuma bukaci mambobin da abun ya shafa da su daina daukar kansu a matsayin yan jam’iyya ko su fuskanci hukunci.
Daya daga cikin mambobin da abun ya shafa, Okoyooba, wanda ya tabbatar da ci gaban, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa za su hadu domin sanin mataki na gaba da za su dauka.
A watan Okotoba, Omoyooba ya jagoranci sauran mambobi wajen yin zanga-zanga domin Allah wadai da yunkurin shugabancin jam’iyyar a jihar na zartar da hukunci game da taron PDP na karshe a jihar.
Kaduna: Isa Ashiru, tsohon dan takarar PDP, ya bayyana niyarsa na sake fitowa takarar gwamna
A wani labari na daban, dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Hon Isa Kudan Ashiru ya ce shi ya samu nasara a zaben 2019 amma magudi aka tafka masa, amma zai kara tsayawa takarar a shekarar 2023, Vanguard ta ruwaito.
Ya kara da cewa yana siyasa ne don yi wa mutane aiki sannan ya shayar da jama’ansa romon dimokradiyya.
Ita ma The Cable ta rahoto cewa Dan siyasar ya bayyana kudirinsa yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna inda ya ce zai kara tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar PDP kuma a cewarsa babu gudu babu ja da baya.
Asali: Legit.ng