Ganduje: A Shirye Na Ke In Yi Sulhu Da Sanata Kwankwaso

Ganduje: A Shirye Na Ke In Yi Sulhu Da Sanata Kwankwaso

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce a shirye ya ke da ya shirya da wanda ya gaji mulkin Kano a hannunsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • A wata tattaunawa da Radio France ta yi da shi, gwamnan ya kwatanta rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu a matsayin sabanin siyasa
  • Ganduje ya ce wannan sabanin ba wani abu bane sabo don ya saba faruwa kuma da yardar Ubangiji yadda ya zo zai wuce don shirin ya fi zama alheri

Jihar Kano - Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya ce a shirye ya ke da ya gyara alakar da ke tsakaninsu da sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa wacce Radio France ta yi da gwamnan ya kwatanta rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu da Kwankwaso tsakanin sabani.

Kara karanta wannan

Sanata Kwankwaso ya yi magana game da ta’aziyyar da Ganduje ya zo ya yi masa har gida

Ganduje: A Shirye Na Ke In Yi Sulhu Da Sanata Kwankwaso
Ganduje ya ce a shirye ya ke ya yi sulhu da Kwankwaso. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kamar yadda ya ce:

“Kun san akwai masu hura wa rigima wuta. Don haka yanzu haka muna kokarin ganin mun dakatar da su tare da gyara alakarmu.
“Irin wannan fadan ya dade yana faruwa ba sabon abu bane kuma zai wuce. Kowa ya san sulhu ya fi komai zama alheri. Muna fatan Ubangiji zai taimaki masu kokarin shirya mu.
“A wurinmu kuwa, a shirye muke da mu hada kai don shiryawa. Ba wai mun ki bane. Akwai masu rura wuta ko ta ina, amma na ce duk abinda aka yi amfani da hankali wirin aiwatar da shi ina ganin zai wuce.”

Ganduje ya je gidan sanatan don ta’aziyya ranar Talatar da ta gabata

A ranar Talata, Ganduje ya je yiwa Kwankwaso ta’aziyya, a gidansa da ke Bompai, layin Miller akan mutuwar dan uwansa, Inuwa Musa Kwankwaso, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

A Bompai, Sanatan da sauran ‘yan jam’iyyarsu sun amshi gwamnan hannu bibbiyu.

Cikin wadanda su ka raka gwamnan akwai shugaban ma’aikatansa, kwamishinoni da dama, shugabannin jam’iyyar da sauran manya masu mukamai a gwamnati.

Har kabarin mahaifinsa Kwankwaso ya kai Ganduje

Kwankwaso ga gayyaci gwamnan har zuwa kabarin mahaifinsa, Musa Saleh Kwankwaso, wanda ya ke cikin gidan sanatan inda aka ci gaba da addu’o’i.

Malamai da dama sun dinga yiwa mamacin addu’a daga bisani su ka raka gwamnan bayan kwashe fiye da mintoci talatin tare da shi.

Sanata Kwankwaso ya yi magana game da ta’aziyyar da Ganduje ya zo ya yi masa har gida

A wani labarin mai alaka da wannan, Tambari TV Hausa tayi hira da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a game da rashin da aka yi masa a farkon makon nan na Inuwa Musa Kwankwaso.

Da yake zantawa da manema labaran, da farko ‘dan siyasar ya fara da maganar rashin ‘danuwa da ya yi, ya na mai yabon Marigayi Inuwa Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba

Rabiu Musa Kwankwaso yace daga Ubangiji Madaukakin Sarki muke, kuma gare shi za mu koma. Kwankwaso yace 'danuwan na sa ya samu shaidar mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164