Ganduje ya yi bayanin rigimarsa da su Shekarau a APC, yace Jam'iyya za tayi masu sulhu

Ganduje ya yi bayanin rigimarsa da su Shekarau a APC, yace Jam'iyya za tayi masu sulhu

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana inda ake ciki a rikicin cikin gidan APC
  • Abdullahi Umar Ganduje yace uwar jam’iyya ta tsoma bakinta domin a samu masalaha a jam’iyya
  • Dr. Ganduje yake cewa dole a rika hakuri da juna a siyasa, kuma ya na sa ran a samu jituwa a APC

Kano – Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan sabaninsa da bangaren Malam Ibrahim Shekarau a rikicinsu na cikin gidan APC.

Da aka yi hira da shi a RFI Hausa, mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sam ba wani abin mamaki ba ne don an samu rashin jituwa a siyasa.

A cewar Dr. Abdullahi Ganduje, uwar jam’iyya ta na kan kokarin sasanta wannan rikicin cikin gidan.

Kara karanta wannan

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

“Ana nan ana sasantawa, kamar yadda ka sani, uwar jam’iyyar ta shiga. Kuma samun rabuwar kai a siyasa ba sabon abu ba ne, a daidaita ba sabon abu ba ne.”
“Saboda haka duka masu wannan, da dukkanmu ‘yan siyasa ne, mun san wani lokaci za a bata, wani lokacin kuma sai a shirya.” – Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Gwamna Ganduje ya dade a wannan harkar

Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021, Abdullahi Ganduje yace ba yau ya fara siyasa ba, gwamnan yace ya dade a wannan harka.

“Amma abin da muke cewa shi ne, wannan siyasa ba wai mun tsince ta a bakin titi ba ne. Mun shige ta ne fiye da shekara 40 da suka shige.”

Kara karanta wannan

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

“Kuma bugu da kari ma, ita mu ka karanta a jami’a, kuma ita mu ke yi. Saboda haka mun san siyasa harka ce ta hakuri.” – Gwamna Ganduje.

Hakarmu za ta cin ma ruwan sha - Ganduje

A jawabin na sa, gwamnan na Kano yace ba a yin abokin gaba da din-din a siyasa, sai dai ma abokin din-din-din saboda yadda mutane suke canza alkibla.

A karshe Abdullahi Ganduje yace ya na sa ran hakarsu za ta cin ma ruwa wajen sasanta ‘yan APC.

Rikicin cikin gidajen APC

A Kano abin ya yi kamari tsakanin Abdullahi Ganduje da tsaginsu Ibrahim Shekarau da Barau Jibrin. Rashin jituwar ta jawo aka samu shugabanni biyu a Kano.

Bangaren gwamnati su na tare da Abdullahi Abbas yayin da su Shekarau ke tare Ahmadu Danzago.

Asali: Legit.ng

Online view pixel