Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba

Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba

  • Tsohon kwamishina a jihar Cross Riba tare da wasu jiga-jigan APC sun koma jam'iyyar hamayya PDP
  • Tsohon gwamna, Donald Duke, da wasu shugabannin PDP a jihar ne suka tarbi masu sauya shekan a sakateriyar PDP dake Kalaba
  • A cewar ɗaya daga cikin tsaffin yan APC ɗin, komawarsu PDP tamakar komawa gida ne domin daman nan ne asalin su

Calabar, Cross River - Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, tare da manyan jiga-jigan PDP sun karbi tawagar masu sauya sheka daga APC.

Manyan jiga-jigan APC mai mulki a jihar da suka haɗa da Honorabul Ekbo Okon, Honorabul Wilson Ekpeyong, Honorabul Paul Ogar, Ntufam Asu E. da wasu mutum biyu sun koma tsagin hamayya na PDP.

Da yake jawabi a sakateriyar PDP dake Kalaba, Duke, ya nuna farin cikinsa da kuma maraba ga sabbin mambobin jam'iyya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari

Jam'iyyar PDP
Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan yace karban masu sauya sheka daga APC yanzun aka fara, ya tabbatar da cewa akwai sauran rukunin waɗan da zasu dawo PDP ba da jimawa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta rahoto Duke yace

"Ba zamu lamurci sadaukar da basirar mu ga wasu ba, ya kamata su dawo gida mu haɗa kai mu gyara gidan."
"Idan baki ɗaya masu son dawowa PDP zamu karbe su yau, sakateriyar nan ba zata ɗauke mu ba. Dan haka mun yanke hukuncin karɓan su a rukuni-rukuni."

Mun ji dadin dawowa gida

Da yake jawabi a wurin taron, tsohon kwamishina, Ekpo Ekon, ya gode wa Allah bisa dawowarsa jam'iyyar PDP, tare da tabbatar da cewa ya dawo gida.

Yace:

"Ina godiya ga Allah da ya nuna mun wannan rana, da kuma waɗan da suka jajirce wajen rike wannan jam'iyya. Dawo wa na PDP tamkar dawowa gida ne."

Kara karanta wannan

Sauya shekar kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP ba zai canza komai ba, Jam'iyyar APC ta yi Martani

"Wani lokacin kana ficewa daga gida, a kira ka kuma ka dawo. Naji kiran ku daga kowane lungu da saƙo na Kalaba da kuma daga kowanne daga cikin ku."

Akwai sauran masu dawowa PDP - Shugaban PDP

Tun da farko, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Venatius Ikem, ya tabbatar da cewa daga nan zuwa watan Maris na shekara mai kamawa, akwai dandazon waɗan da zasu dawo PDP.

"Kunsan yanzun muna cikin lokacin kawo amfanin gona gida ne, sabida haka zamu dawo da mutane da dama gida."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata dauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Jam'iyyar APC tace har yanzun tana dakon kwafi na asali na hukuncin da kotu ta yanke kan zaɓen shugabanni a Kano.

Sakataren APC na kasa, Sanata James, yace jam'iyya zatai nazari kan hukuncin kafin ta ɗauki matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262