2023: Ina fatan Atiku zai goyi baya na kamar yadda na mara masa baya a 2019 - Yul Edochie

2023: Ina fatan Atiku zai goyi baya na kamar yadda na mara masa baya a 2019 - Yul Edochie

  • Jarumin fina-finan Nollywood, Yul Edochie ya ce ya na fatan tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya mara masa baya akan kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
  • Yul, wanda ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar DPC a 2017, a watan Fabrairun da ya gabata ya bayyana kudirinsa na neman shugabancin kasa a 2023
  • A cewarsa, lokacin da Atiku Abubakar ya nemi mulkin Najeriya har daina aiki ya yi daga ma’aikatar gwamnati duk don ya tabbatar da nasararsa

Jarumin Nollywood, Yul Edochie ya bayyana fatansa akan tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubukar na goya masa baya akan burinsa na shugabantar kasa a 2023.

Yul, ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar DPC a 2017, sannan a watan Fabrairu ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

2023: Ina fatan Atiku zai goyi baya na kamar yadda na mara masa baya a 2019 - Yul Edochie
Jarumi Yul Edochie ya ce yana fatan Atiku zai mara masa baya kamar yadda shima ya masa a 2019. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

A cewarsa, mahaifinsa, wanda shima jarumin fina-finai ne, Pete Edochie ya goya masa baya akan kudirinsa.

Yul ya sanar da hakan ne ta wani bidiyo da ya wallafa a shafukansa na kafafen sada zumunta.

Yul ya ce cin tuwon kishiya ramako

Kamar yadda yace:

“Mahaifina Chief Pete Edochie ya goya min bayan tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023... Ubangiji mahalicci ya taimaka mana.”

Yayin da 2023 take matsowa, jarumin wanda ya samu albarkar mahaifinsa ya bukaci goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa wanda ya tsaya mawa a lokacin kamfen dinsa a 2019.

Har dakatar da aiki ya yi don yin kamfen din Atiku

Yul Edochie ya wallafa kamar yadda The Nation ta nuna:

“A shekarar 2019 na nuna goyon baya ga Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa. Kuma nayi hakan ne cike da jajircewa da alfahari.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

“Har dakatar da aikina na yi don in bai wa Atiku Abubakar goyon baya ba tare da wani abu ya dakatar da ni ba. Kuma na yi hakan ne don tallafa wa kasar nan.
“Sai da nasa duk dan jihar Anambra ya bi Atiku. Matasan Najeriya ma duk suka bi ni don mu tsaya wa Atiku. Amma kuma lamarin sai bai tabbata ba.”

Wannan karon ‘yan kudu maso gabas ne zasu samar da shugaban kasa

Kamar yadda yace, wannan karon bangaren kudu maso gabashin kasa ne ya kamata su samar da shugaban kasa. Kuma ya bayyana ra’ayinsa na son tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023.

Ya ce yana fatan Atiku ya mara masa baya kamar yadda ya yi masa a baya. Sannan ya yi addu’ar Ubangiji ya taimaki wannan kasar tamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel