Labari cikin Hotuna: Yadda Yan daba suka kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau a Kano
- Wasu gungun yan daba sun kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin tsohon gwamna, sanatan Kano ta tsakiya, Malam Shekarau
- Rahoto ya nuna cewa yan daban sun kai wannan hari ne da yammacin Ƙaraba, inda suka kona sakateriyar dake hanyar Maiduguri a Kano
- A halin yanzun jami'an tsaro sun mamaye ofishin domin shawo kan lamarin da tabbatar da zaman lafiya
Kano - Rahoton da muke samu yanzu haka daga jihar Kano dake arewacin Najeriya ya nuna cewa gungun yan daba sun kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin shekarau.
Wani mazaunin Kano, Musbahu Rabiu Gyadi-Gyadi, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa yan daban da suka kai harin sun kai mutum 500.
Wannan na zuwa ne kwana kaɗan bayan kotu ta rushe shugabannin APC na bangaren gwamna Ganduje na jihar Kano, sannan tabbatar da bangaren Malam Shekarau.
Yadda lamarin ya faru
Rahoto ya nuna cewa ɗaruruwan yan daba sun kai harin ofishin wanda ke kan hanyar Maiduguri da yammacin ranar Laraba.
Ginin da abun ya shafa mallakin tsohon ministan kwadugo ne, Alhaji Musa Gwadabe.
A halin yanzun jami'an yan sandan jihar Kano sun mamaye sakateriyar APC ta tsagin Shekarau, domin shawo kan lamarin.
Da muka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace yana cikin taro ne a lokacin.
Hotunan sakateriyar APC
Legit.ng Hausa ta tattaro muku abinda wasu yan siyasa a jihar Kano ke cewa dangane da wannan lamarin.
Wani ɗalibi a jami'ar BUK, kuma mai bibiyar al'amuran siyasa ɗan asalin jihar Kano, Honorabul Hafeez Kiido, yace:
"Yanzu tsarin siyasar da ake kira kyan-kyasar siyasa shine wannan? Ashe haka demokaraɗiyyar take? Kawai dan wasu sun ɗauki layi daban da gwamnati a siyasance, sai a kone musu waje a nemi cutar da su kuma abun kunya da yan daba."
"Akwai takaici sosai tsarin siyasar Kano, tabbas babu kwayar zarra ta ilimi a wannan aiki. Kuma wannan ƙara bude kofar dawo da siyasar daba ce irin ta 2003-2007 a Kano."
Da muka zanta da wani ɗan siyasa a tsagin Ganduje, wanda ya nemi a sakaya sunansa yace:
"Wato abinda ke faruwa a Kano tsakanin Ganduje da Shekarau ya yi tsanani, amma a mahanga ta bangaren Shekarau ne suke da gaskiya, sun fi Ganduje gaskiya."
"Bara na fito maka ɓaro-baro, bangaren Ganduje suna da hannu a harin da aka kai ofishin sanata Barau, kawai dai Ganduje ba shi da masaniya, amma yan tsaginsa ne suka yi haka domin ɗaukar fansa biyo bayan hukuncin kotu."
"Ba ta yanda za'ai abinda kotu ta yanke ya yi wa ɓangaren Ganduje daɗi, lokaci daya aka ce an rushe zaɓen su Abdullahi Abbas, kuma an tabbatar da na tsagin Shekarau, ai dole abun ya musu ciwo. Kawai siyasar Kano sai Kano."
A wani labarin kuma Gwamnatin Kano tare da yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a ofishinsa
Jami'an ma'aikatar filaye tare da jami'an yan sanda a Kano sun rufe ofishin lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a shari'ar shugabancin APC.
Nureini Jimoh, SAN, ya tabbatar da rufe ofishinsa da aka yi yana mai cewa shi da wasu ma'aikatansa suna ciki yayin da aka garkame kofar ofishin.
Asali: Legit.ng