Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra

Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra

  • Babbar kotun Abuja ta yanke hukunci, ta yi watsi da karar da aka shigar kan zababben gwamnan Anambra
  • Kotun ta ce ba ta gamsu da bayanan da masu shigar da kara suka gabatar ba, don haka ta kori karar
  • An shigar da karar Soludo da mataimakinsa ne bisa zargin ba da bayanan karya ga hukumar zabe ta INEC

Abuja - The Nation ta ruwaito cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ta nemi a soke takarar gwamna da mataimakan gwamna na jam’iyyar APGA a zaben gwamnan da ya gabata a jihar Anambra.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, karar an shigar da ita kan dan takarar APGA da ya lashe zabe, Charles Soldu da mataimakinsa Onyeka Ibezim.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Masu shigar da kara – Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka – suna zargin Soludo da Ibezim sun bayar da bayanan karya a cikin takardar da suka mika wa hukumar INEC don haka a bayyana cewa ba su cancanci tsayawa takara ba.

Solud da Ibezim
Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori karar da ke neman Soludo, Ibezim ya hana shi takara | Hoto: thenigerianvoice.com
Asali: UGC

A cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/711/2021 masu shigar da kara sun yi ikirarin cewa Soludo ya nuna a cikin fom dinsa na EC9, Aguata 2 ita ce mazabar da a Anambra ya ke takara, yayin da hakikanin gaskiya, ya tsaya takarar gwamnan Anambra.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce Ibezim ya nuna sha'awar tsayawa a Awka 2 a Anambra a matsayin kujerar gwamnan da yake takara, kamar yadda TVC ta ruwaito.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, Mai shari’a Taiwo Taiwo ya ce karar ba ta da tushe, domin wadanda suka shigar da karar sun kasa nuna yadda aka yaudare su da bayanan da Soludo da Ibezim suka bayar.

Kara karanta wannan

An dakatad da Shugaban APC a Anambra kan laifi 'ya yiwa Buhari rashin kunya

Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, Soludo da Ibezim sun nuna sha'awar karara a kan mukaman gwamna da mataimakinsa a fom din da suka mika wa INEC kawai dai sun fadi mazabarsu ne, kuma hakan ba ba da bayanan karya bane.

Alkalin kotun ya ce kowa ya sani, ciki har da masu kara, cewa zaben gwamna ne kawai aka gudanar a Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamban wannan shekara.

Ya warware duk wasu batutuwan da aka gabatar daga masu shigar da kara kuma ya ki ba da duk wani taimako da suke nema.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ba da kyautar Naira miliyan 2 ga wadanda suka shigar da kara, sannan su ba APGA, Soludo da Ibezim goyon baya.

Wadanda ake tuhumar sun hada da INEC, jam'iyyar APGA, Soludo da mataimakinsa Ibezim.

Zaben Anambra: Wa'adin shigar da kara ya kusa karewa, APC ba ta shigar da kara ba

Kara karanta wannan

An hana yaron Marigayi Muammar Gaddafi neman kujerar Shugaban kasa a zaben Libya

A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa, saura kwanaki shida a cika wa’adin gabatar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ba ta karbi batun ba daga wata jam'iyya ba har yanzu.

A cewar dokar, ‘yan takara da jam’iyyunsu da suka sha kaye suna da hurumin kwanaki 21 daga ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da zabe domin su gabatar da kara.

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne jami’ar kula da zabe na jihar Anambra, Farfesa Florence Obi, ta ayyana Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.