Buhari zai gyara Najeriya tsaf kafin ya sauka a mulki a zaben 2023, inji Sanata
- Sanata Ibikunle Amosun ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar mulki a 2023 a matsayin jarumin kasa
- Amosun, wanda ya dade yana goyon bayan shugaban kasa a siyasance, ya yi wannan tsokaci ne a wani bikin karrama shi
- Wani mutum Mista Taiwo Adeoluwa ne ya wakilci tsohon gwamnan jihar Ogun a wajen taron karramawar
Ibadan – Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya, Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara gyara kasar nan kuma zai bar mulki a 2023 a matsayin jarumin kasa.
Amosun ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake kwatanta yadda jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta shafe shekaru shida tana mulki da kuma yadda jam’iyyar PDP ta yi mulki na shekaru goma sha shida a kasar.
Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Amsoun, kwararren akanta ya bayyana hakan a yayin wani taron tunawa na bikin mako na shekara ta 2021 na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a jihar Oyo a Ibadan.
Ya bayyana cewa Najeriya ta samu kyakykyawan ci gaba a mulkin Buhari na shekaru shida kuma ci gaban da aka samu a bayyane yake ga kowa.
Ya kara da cewa al’amuran da suka dabaibaye kasar nan musamman tabarbarewar tsaro sune sakamakon rashin iya mulkin PDP na tsawon shekaru goma sha shida, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa shugaba Buhari baya domin ya ci gaba da magance matsalar.
A cewarsa:
“Ayyukan noma da ababen more rayuwa sune babban abin da gwamnatin Buhari ta maida hankali akai. Manoma sun sami tsarin lamuni mai sauki fiye da da. An dauki tsarin layin dogo na Najeriya a matsayin mafi muni a Afirka kafin hawan Buhari a 2015.
“Buhari ya kaddamar, ya kammala tare da samar da manyan hanyoyin layin dogo, kuma a yanzu Najeriya tana da tsarin layin dogo mafi kyau a Afrika ta Yamma tare da samar da dubunnan ayyukan yi.
Kana, sanatan ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abubuwan da gwamnatocin baya suka gaza yi a kokarinsa na kawo ci gaba da kasar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
A cewarsa:
"Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar kasar nan alheri da yawa kuma idan ya bar mulki a 2023, zai bar abubuwa fiye da gwamnatin da ta gabace shi aiki."
Amosun, wanda Mista Taiwo Adeoluwa ya wakilta a wajen taron, an kuma karrama shi da lambar yabo ta Nation’s BridgeBuilder and Icon of Progressive Bloc ta kungiyar NUJ.
Dr Florence Ajimobi, matar tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Sanata Abiola Ajimobi ce ta bayar da kyautar.
Sai dai, duk da irin yabon da ya yiwa shugaban kasar, 'yan Najeriya na ci gaba da koka yadda mulkin shugaban kasar yake, musamman a kwanakin nan da gwamnati ta sanar da yiyuwar cire tallafin man fetur.
Wani tsohon sanata daga jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya bayyana irin walhalun da 'yan Najeriya za su shiga idan gwamnati ta cire tallafin na man fetur.
N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000
A tun farko, gwamnatin tarayya ta ce za ta rika kashe N200 billion a wata wajen rabawa talakawan Najeriya kudi domin rage zafin da cire tallafin mai zai haifar.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.
Leadership newspaper ta ruwaito cewa Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne ranar Talata, 23 ga Nuwamba 2023 a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).
Asali: Legit.ng