2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

  • Fitaccen dattijon arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce wannan kokarin ganin raba kasar nan da shugaban 'yan aware, Nnamdi Kanu, ke yi ya na kara rage yuwuwar samun dan takara nagari daga yankin
  • Yakasai ya ce, ba shi da matsala kan yunkurin karbar mulkin kasar nan da kudu ke yi, kawai abinda ya dace shi ne su tashi tare da nuna cewa za su iya ba wai mulkin ya same su a zaune ba
  • Dattijon ya ce, tabbas burin karbar mulki ya na tattare da 'yan kudu maso gabas din, amma kuma babu wata alama da ke nuna cewa za su iya samun mulkin tunda sun kalmashe kafa ne

Kano - Daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Arewa Consultative Forum kuma dattijon arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce kokarin ganin rabewar kasar nan da shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu ya saka gaba, ya kara rage yuwuwar samun shugabancin dan kabilar Ibo a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da Channels TV a ranar Lahadi.

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai
2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda tsohon mai shekaru 96 yace, dole ne yankin kudu maso gabas na kasar nan su gamsar da 'yan Najeriya cewa sun shirya karbar mafi darajar ofishin siyasan kasar nan a 2023.

Kanu, wanda ke hannun hukumar tsaro ta farin kaya, ya na fuskantar zargi kan ta'addanci da cin amanar kasa a gaban Mai shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Shi da kungiyarsa sun zargi cewa ana ware kabilar Ibo a bangaren shugabanci, rashin tsaro, daga cikin dalilansu na bukatar a raba kasar.

A yayin da zaben 2023 ke tunkarowa, yankin kudu maso gabas na cigaba da son karbar mulki inda kungiyoyi irinsu Ohanaeze Ndigbo, gwamnoni biyar na kudu maso gabas ke kira kan cewa yankinsu ya dace ya samar da shugaban kasa na gaba bayan cikar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ke dan asalin Daura ne a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Ohanaeze da gwamnonin da suka samu jagoranci Dave Umahi na jihar Ebonyi, sun yi ikirarin cewa babu shugaban kasar Najeriya da aka taba samu dan yankin tun bayan dawowar mulkin damokaradiyya a 1999, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan siyasa daga yankin kudu maso gabas tuni suka fara komawa jam'iyyar APC da PDP domin samun damar fitowa takara da nasarar darewa kujerar shugabancin kasa.

A yayin jawabi a tattaunawar, Yakasai ya ce bai dace kabilar Ibo ta kalmashe kafa kuma ta na bukatar a mika wa yankin mulkin kasa ba.

Ya ce, "Wuka da nama ya na hannun jama'ar kudu maso gabas. Ya rage garesu da su yi amfani da shi. Ina matukar goyon bayan a mika mulkin kasa hannun dan kudu bayan Buhari kuma ko kudu maso gabas aka bai wa mulki, ba ni matsala.
"Matsala ta daya shi ne, wannan ba abu bane fa za ka zauna a gida ka yi addu'a a kai. Dole ne ku tashi ku nuna za ku iya, ku zaburo kuma ku nuna wa jama'a tabbas za ku iya daukar nauyin. A tunani na wannan ne 'yan kudu maso gabas suka rasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau

"Akwai burin tattare da su amma kuma sun kasa bayyanawa kuma sun kasa ganar da mutane cewa za su iya.
"Tabbas 'yan Najeriya sun damu da matsayar kudu maso gabas saboda abun mamaki ga mutane iri na. Duba kamar wannan Nnamdi Kanu wanda ko dan takarar gwamna bai cancanta ba, amma ya na kokarin samun goyon baya daga fitattun 'yan kudu maso gabas.
Wannan ke sa muke tantamar anya kuwa sun shirya samar da dan takarar da zai taimaki Najeriya gaba dayan ta? Ina tantama gaskiya."

Dattawan Arewa ga Buhari: Kada ka kuskura ka yafewa dan awaren nan Nnamdi Kanu

A wani labari na daban, kungiyar Dattawan Arewa (NEF), a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da bukatar wasu fitattun shugabannin Igbo, inda suka bukaci a sako Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB.

Kungiyar ta bayyana cewa babu wani dalili na aminci, ingantacce ko kuma sanin makamar amincewa da bukatar, kuma ta shawarci shugaban kasa da kada ya jinkirta bayyana cewa za a bar tsarin shari’a yayi aikinsa akan Kanu.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

Dattawan sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ta, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kuma Legit.ng ta gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng