'Yan APC a Arewa sun fara gangamin nuna goyon baya ga Okorocha ya zama shugaba a 2023
- Kungiyar magoya bayan APC a Arewa sun fara gangamin nuna goyon baya ga Sanata Rochas Okorocha domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
- Kungiyar ta yi ikirarin cewa babu wani dan Najeriya da ya bayar da irin gudunmawar da Okorocha ya bayar wajen ci gaban Arewa a baya-bayan nan
- Ta kuma bayyana cewa tsohon gwamnan zai hada kan Arewa da Kudu saboda ya fahimci al’adun mutanen Arewa da mutanen Gabas sosai
Kano - Wata gamayyar kungiyoyin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a fadin arewa sun kaddamar da gangamin nuna goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, domin ya zama shugaban kasa a 2023.
Jaridar Sun ta rahoto cewa, taron wanda ya gudana a jihar Kano, ya ja hankalin magoya baya da masu biyayya ga jam'iyyar da kuma wakilan kungiyoyi masu zaman kansu a fadin arewa.
Da yake magana a dakin taron na Menna Event Centre, jagoran kungiyar na kasa, Sadiq Abubakar ya tabbatar da cewa babu wani dan Najeriya da ya bayar da irin gudunmawar da Okorocha ya bayar wajen ci gaban Arewa a baya-bayan nan.
Ya bayyana cewa Okorocha ta gidauniyarsa, ya taba rayukan 'yan arewa da dama ta hanyar kafa makarantun kyauta ga marayu da marasa karfi a jihohin Kano, Kaduna, Sokoto, Bauchi, Jos da Adamawa.
Ya kara da cewa a wadannan makarantu, ana raba inifam ga dalibai a kyauta sannan ana ciyar da su ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.
Yayin da yake tunatar da cewa Okorocha ya iya tsantsar Hausa, ya bayyana cewa arewa ta yarda da Okorocha, musamman saboda hadin kan Najeriya zai samu a karkashin kulawarsa.
Ya ce:
"Shi mutum ne mai hada kan Arewa da Kudu saboda fahimtar al’adun mutanen Arewa da mutanen Gabas."
Da take magana a taron, shugabar matan kungiyar, Jamila Abdullahi ta roki yan arewa musamman mata da su marawa takarar shugabancin Okorocha baya.
Ta ce da tarin kwarewarsa, zai ceto Najeriya daga halin da take ciki a yanzu na kalubalen siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro, jaridar Independent ta rahoto.
2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari
A wani labarin kuma, tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kan kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Saraki wanda yayi ganawar sirri da Ortom ya kuma gana da kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP a jihar domin sanar da su kudirinsa na fara tuntuba game da aniyarsa na shugabantar kasar, rahoton Daily Trust.
Ya bayyana cewa sauya shekar da masu biyayya ya jam’iyyar All Progessives Congress (APC) ke yi zuwa PDP a fadin kasar alamu ne da ke nuna cewa jam’iyyar na iya zama babu kowa kafin zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng