2023: Kada ku zabi jam'iyyar PDP, ku zabi wanda na yarda da shi, Gwamna El-Rufa'i ya roki yan Najeriya

2023: Kada ku zabi jam'iyyar PDP, ku zabi wanda na yarda da shi, Gwamna El-Rufa'i ya roki yan Najeriya

  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya gargaɗi yan Najeriya musamman mutanen Kaduna kada su zabi PDP a 2023
  • El-Rufa'i ya roki al'ummar jihar Kaduna su yarda da shi, zai zabar musu wanda ya dace ya gaji kujerarsa a 2023
  • Ya kuma caccaki Sanata Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi bisa abinda ya kira durkusad da cigaban Kaduna

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya roki al'ummar jihar Kaduna kada su zabi jam'iyyar PDP a baban zaɓen 2023 dake tafe.

Vanguard ta rahoto Gwamnan na cewa matukar mutane suka zabi PDP to zata maida Najeriya gidan jiya ne.

Gwamnan ya yi kira ga yan jihar da su amince masa kuma su tabbatar sun zabi duk mutumin da ya nuna musu ya gaji kujerarsa ta gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Gwamna El-Rufai
2023: Kada ku zabi jam'iyyar PDP, ku zabi wanda na yarda da shi, Gwamna El-Rufa'i ya roki yan Najeriya Hoto: dailynugerian.com
Asali: UGC

El-Rufa'i ya yi zargin cewa badan halayyan tsoffin sanatocin jihar, Shehu Sani da Sulaiman Hunkuyi ba da tuni cigaban da gwamnatinsa zata kawo ya zarce haka.

Ya kuma bada misali da gadar kawo, inda yace ba shi kaɗai mutane zasu yaba wa kan aikin ba, harda yan majalisun tarayya, waɗan da suka tabbatar majalisa ta amince an yi aikin.

Me tsofaffin sanatocin suka yi?

Bugu da kari gwamnan ya bayyana cewa matakin da su Shehu Sani da Saulaiman Hunkuyi suka ɗauka a baya ya durkusan da cigaban Kaduna.

Bisa haka ya zama wajibi mutanen Kaduna su natsu, kuma kusan wa zaku zaɓa, domin guje wa kawo makiyan Kaduna su lalata komai, inji gwamnan.

"Fushin Allah ya tabbata akan su," El-Rufa'i yayi addua, yayin da dandazon mutane suka amsa da Ameen a Ahmadu Bello Stadium.

Kara karanta wannan

Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a wurin taron kaddamar da sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga na jihar Kaduna.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga 'Sardaunan Kano'

Idan baku manta ba, manyan jiga-jigan APC biyu sun fara taƙaddama da juna a lokacin gangamin taron jam'iyya na jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda kowane tsagi tsakanin gwamna Ganduje, da Sanata Ibrahim Shekarau ya fitar da shugaban APC a matakin jiha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262