Jerin jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaben kananan hukumomin wannan jihar, babu PDP a ciki
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ekiti ta bayyana sunayen jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaɓen kananan hukumomi dake tafe
- Sai dai ga dukkan alamu, babu babbar jam'iyyar hamayya PDP a cikin jerin sunayen da hukumar SIEC ta fitar ranar Talata
- Kwamishinan yan sandan jihar, Mr. Tunde Mobayo, ya gargaɗi masu tada kayar baya kada su shiga harkokin zaben dake tafe
Ekiti - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Ekiti, (SIEC), Justice Jide Aladejana, yace jam'iyyun siyasa 6 ne kacal zasu fafata a zaɓen kananan hukumomin jihar.
Dailytrust ta ruwaito cewa hukumar SIEC ta shirya gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar Ekiti ranar 4 ga watan Disamba, 2021.
Shugaban hukumar zaben ya bayyana sunayen jam'iyyun kamar haka:
"Jam'iyyar All Progressives Congress(APC), jam'iyyar Young Progressives Party (YPP), Jam'iyyar AA, jam'iyyar PRM da kuma jam'iyyar ADC."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane shiri hukumar zaben ta yi?
Aladejana yace hukumarsa zata gudanar da zaben ciyamomi da na kansiloli a kananan hukumomi 16 da aka sani a doka, da kuma sabbin yankuna 19 da a ka kirkira karkashin (LCDA).
Bugu da kari, ya tabbatar da cewa hukumarsu da kuma hukumomin tsaro sun kammala duk wasu shirye-shirye domin gudanar da sahihin zabe.
A cewarsa babu wanda za'a amince ya gurgunta namijin kokarin gwamnati na tabbatar da tsarin shugabanci a mataki na uku.
Aladejana ya bayyana haka ne ranar Talata a Ado Ekiti, yayin da yake ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa kan zaben dake tafe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wane shiri jami'an tsaro suka yi?
A nasu ɓangaren, rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti, ta bayyana cewa ba zata bar wasu masu mummunan nufi su tada hankali ba yayin zaben.
Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno
Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr. Tunde Mobayo, ya gargaɗi duk masu shirin tada hargitsi kada su yi kuskuren zuwa wurin zaɓe.
A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga sarautan 'Sardaunan Kano'
Idan baku manta ba, manyan jiga-jigan APC biyu sun fara taƙaddama da juna a lokacin gangamin taron jam'iyya na jihar Kano.
Yayin da tsagin gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, shi kuma Shekarau ya bayyana Alhaji Haruna Danzago a matsyain shugaba.
Asali: Legit.ng