Buni ya bayyana dalilai 5 da suka sanya Buhari kai babban taron APC watan Fabrairun 2022
Shugabancin APC ya yi bayanin dalilin da yasa ba za a iya gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a 2021 ba da kuma abun da ya sa aka kai taron watan Fabrairun 2022 kamar yadda aka amince tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ne yayi bayanin a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba.
Bayanin na Buni na zuwa ne bayan wani taro da ya samu halartan gwamnonin APC karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da shugaban kasa a fadar Villa.
Ga jerin dalilan da suka sanya aka daga babban taron a kasa:
1. Rikice-rikicen APC a jihar Anambra
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Rashin kwanciyar hankali da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Zamfara
3. Kalubalen kayayyaki
4. Shirye-shiryen hutun kirsimeti
5. Zaben gwamnan jihar Ekiti mai zuwa
Wani bangare na jawabin Buni game da abubuwan da aka lissafa a sama kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto:
“Na kuma yi bayani a jiya cewa kungiyar gwamnonin APC sun tattauna kan lamarin babban taron jam’iyyar na kasa kuma sun bukacemu da mu zo mu tattauna da shugaban kasa a matsayinsa na shugaban jam’iyya domin mu ba da shawarwarin gwamnoni don jam’iyyar da shugaban kasa su duba.
“Daga cikin shawarwarin da muka samu a jiya shi ne cewa muna da jihohi shida, wadanda suke a matakin kamala tarukansu kamar Anambra, bisa fahimta saboda zaben gwamna da aka yi kwanan nan, Zamfara da wasu biyu, saboda kalubalen kayan aiki sannan kuma, bikin Kirsimeti na kan hanya kuma a farkon Janairu za mu mayar da hankali kan Ekiti sosai.
“Saboda haka, gwamnonin, sun yi la’akari da wadannan, suka bayar da shawarar cewa jam’iyyar da shugaban kasa su duba watan Fabrairu, kuma shugaban kasa ya yi amanna da shawarar."
Shugaba Buhari ya tsayar da lokacin da za a yi taron gangamin APC na kasa
A gefe guda, mun kawo a baya cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar da za ta gudanar da babban taronta na gangami a watan Fabrairu, 2022, The Nation ta ruwaito.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PGF Gwamna Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bagudu ya gana da shugaban kasa da shugaban kwamitin rikon kwarya Mai Mala Buni da takwaransa na Jigawa Mohammed Badaru.
Asali: Legit.ng