Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya magantu a kan abun da suka tattauna da Sanata Orji Uzor Kalu a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba
  • Tinubu ya ce sun tattauna ne a kan lamuran da suka shafi ci gaban kasar Najeriya
  • Ana zaton tsohon gwamnan na jihar Lagas na so ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023

Abuja - Babban jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu a gidansa na Abuja a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba.

Tinubu wanda ake ganin yana zawarcin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ya isa gidan Kalu da misalin karfe 4:25pm sannan ya tafi da misalin karfe 6:45.

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja
Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana cewa ganawar ta su ta karkata ne kan ci gaban kasar, rahoton Premium Times da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja

Tinubu ya ce:

"Mun tattauna “Mun tattauna kan yadda kasar nan za ta ci gaba sannan kasar nan tana da muhimmanci kuma ta fi kowane buri na mutum girma.
“Mun kasance a tare sannan kuma mun damu da kwanciyar hankali, ci gaba, bunkasa da tsaron kasar.
“Makomar matasanmu tana da mahimmanci fiye da duk wasu buruka da san kai da ra'ayin kai."

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

A wani labarin, mun ji cewa akalla sarakunan gargajiya sama da 300 daga kudu maso yamma ne ke goyon bayan takarar tsohon gwamnan jihar Lagas, Sanata Bola Tinubu, a zaben shugaban kasa na 2023.

Sanata Dayo Adeyeye, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne ya bayyana hakan a Gbongan, jihar Osun, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar mai suna ‘South West Agenda for Asiwaju for 2023’ a mazabar Irewole.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng