Zaben 2023: Wajibi jam'iyyar PDP ta kai takarar shugaban ƙasa Arewa saboda abu biyu, LA
- Wani jigon jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, ya bayyana cewa wajibi ne jam'iyyar PDP takai takarar shugaban ƙasa Arewa
- Lawal Usman, wanda aka fi sani da Mista LA, yace yana da manyan dalilan faɗin haka matukar jam'iyyar na son komawa kan madafun iko
- Ya kuma tabbatar da cewa matukar ana son sake lashe zaɓe a PDP, to a tsayar da ɗan arewa saboda yawan magoya baya
Zaria, Kaduna - Jigon jam'iyyar PDP, Lawal Usman, ya bayyana cewa ya zama wajibi PDP ta kai tikitin takarar shugaban ƙasan ta yankin arewa saboda dabarun yaƙi.
Premium times ta rahoto cewa Mista Usman, wanda aka fi sani da 'Mista LA' ya yi wannan furuci ne a Zariya, yayin da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Lahadi.
Mista LA yace:
"Saboda dabaru da kuma amfanin jam'iyya da ƙasa baki ɗaya, ya zama wajibi PDP takai tikitin shugaban ƙasa Arewa a babban zaɓen 2023."
Abubuwa biyu da yasa wajibi PDP takai takara Arewa
Mista LA ya bayyana cewa dalilan da yasa wajibi akan PDP ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa shine saboda adalci da dai-daito.
The Cable ta rahoto Mista LA yace:
"Saboda adalci da kuma baiwa kowane yanki haƙƙinsa, Arewa ya dace ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin PDP."
"PDP ta shafe shekaru 16 a kan madafun iko, yankin kudu maso gabas sun yi jagoranci na shekara 8 ƙarƙashin Obasanjo, kudu maso gudu sun kwashe shekaru 6 karkashin Jonathan."
"Amma baki ɗaya yankin arewa, arewa ta tsakiya, arewa ta gabas da arewa ta yamma sun yi jagoranci na shekara biyu ne kacal karkashin marigayi Yar'adua."
A ina mafi yawan masoyan PDP suke?
Mista Usman, wanda tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya ne, yace PDP ta fi yawan magoya baya a yankin arewa fiye da sauran sassan ƙasar nan.
"Adadin magoya bayan PDP da ake da su a baki ɗaya sassan arewa kaɗai sun isa a duba a baiwa yankin tikitin takarar shugaban ƙasa."
"Idan muna son PDP ta farfaɗo to wajibi mu lashe zaben 2023, kuma idan muna son cimma haka sai an kai tikiti arewa."
"Ina da yakinin cewa zamu samu nasara a zaɓen dake tafe matukar aka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa."
A wani labarin kuma Gwamna Obaseki na PDP ya yi karin haske kan maganar sauya shekarsa zuwa jam'iyyar
A cewar gwamnan, jihar Edo ta shiga wani kangi na kwan gaba kwan baya a cigaba shekaru biyar da suka wuce, amma yanzun ta koma dai-dai.
Obaseki ya tabbatar da cewa ba shi da wani shirin sauya sheka zuwa wata jam'iyya, domin jiharsa ta fusakanci ƙalubale a baya.
Asali: Legit.ng