Duk da inkarin APC, INEC za ta ba Soludo takardar shaidar lashe zaben Anambra

Duk da inkarin APC, INEC za ta ba Soludo takardar shaidar lashe zaben Anambra

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa, za ta ba da takardar cin zabe ga Charles Soludo
  • Charles Soludo ne ya lashe zaben gwamnan da aka kammala a cikin makon nan a jihar Anambra
  • Soludo dan jam'iyyar APGA ya lashe zaben ne da kuri'u sama da dubu dari, lamarin da bai yiwa APC dadi ba

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce za ta gabatar da takardar shaidar lashe zabe ga wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka kammala ranar Juma’a.

INEC ta ce, Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA da mataimakinsa za a ba su takardun shaida a ofishin hukumar da ke Awka, babban birnin jihar, jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da inkarin APC a zaben Anambra, INEC za ta ba Soludo takardar shaidar lashe zabe
Zababben gwamnan Anambra, Charles Soludo | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai taken ‘Zaben Gwamnan Jihar Anambra a 2021’.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Ya ce hukumar ta gana a yau inda ya ce:

"Ta yi nazari na farko kan zaben gwamnan Anambra. Hukumar tana jiran rahoton dukkan jami’an da aka tura domin gudanar da zaben domin yin nazari mai zurfi kan yadda ake gudanar da zaben.
“Bayan kammala zaben kuma kamar yadda yake a sashi na 75 na dokar zabe ta 2010 (wanda aka yiwa kwaskwarima) za’a mikawa zababben gwamnan da mataimakinsa satifiket din takara a gobe Juma’a 12 ga watan Nuwamba 2021 a ofishinmu na jiha da ke Awka."

Hakazalika, hukumar ta INEC ta mika godiya ga dukkan jami'anta da suka yi kokari wajen tabbatar da zaben mai inganci da jami'an tsaro har ma da jama'ar jihar ta Anambra.

A bangaren guda na zaben, kungiyar yakin neman zaben Sanata Andy Uba, dan takarar jam'iyyar APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka kammala.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra

Kungiyar yakin neman zaben ta bayyana sakamakon zaben a matsayin wani abin mamaki, inda ta kara da cewa hakan bai dace da muradin al’ummar jihar ba.

Sai dai, shugaba Buhari, wanda shi ne shugaba a Najeriya kuma mai mulki a karkashin jam'iyyar APC ya amince da sakamakon, inda ya mika sakon taya murna ga Soludo.

Shugaban ya taya Soludo murna ne ta shafinsa na Facebook jim kadan bayan ayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

A bangaren PDP, dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Valentine Ozigbo, a ranar Laraba ya amince da shan kaye tare da taya dan takarar jam’iyyar APGA, Chukwuma Soludo murnar lashe zabe, Punch ta ruwaito.

Soludo mai shekaru 61 ya samu nasara da kuri’u 112,229 inda ya doke Ozigbo wanda ya samu kuri’u 53,807 da Andy Uba na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 43,285 da kuma Ifeanyi Ubah na jam'iyyar YPP da ya samu kuri'u 21,261 wanda ya zo na hudu.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

Ozigbo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce:

"Yanzu na kira Farfesa Chukwuma Soludo na kuma taya shi murnar ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra, 2021. Ina yi masa fatan alheri da kuma yi masa addu'ar samun nasara."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.