Zaben Anambra 2021: Shugaba Buhari na daban ne wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya, Dan majalisa
- Dan majalisar dokokin jihar Legas, Jude Idimogu, yace shugaba Buhari na da hakuri wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya
- A cewarsa sakamakon zaɓen Edo da Ondo, da kuma na kwanan nan a Anambra ya nuna alamun samun cigaba a tsarin zaɓen ƙasar nan
- Ya kuma ya ba wa shugaban bisa yadda gwamnatinsa ta tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali
Lagos - Dan majalisar dokokin jihar Legas, Jude Idimogu, yace shugaba Buhari na daban ne wajen tabbatar da sahihin zabe a Najeriya.
Daily Nigerian tace Ɗan majalisan ya yi wannan furuci ne yayin da yake tsokaci kan zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka kammala cikin nasara.
Mista Idimogu, wanda ya shafe zango biyu yana wakiltar mazaɓar Oshodi-Isolo ta II a majalisar dokokin Legas, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa Buhari ba ya katsalandan a ɓangaren zaɓe.
Yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sakamakon zaɓen gwamnan jihohin Ondo da Edo, da kuma na kwanan nan a jahar Anambra ya nuna cigaban da ake samu wajen tabbatar da an kidaya kuri'un al'umma a tsarin zaɓen ƙasar nan."
"Shugaban ƙasa ya cancanci yabo, yana da hakuri, ba shi da nuna banbanci, a wurinsa duk wanda ya samu nasara zai rungume shi ba tare da banbancin jam'iya ba."
"A koda yaushe ya yarda hukumar zaɓe INEC zata yi abinda ya dace, kuma wannan abu ne mai kyau domin zai ɗaga martabar demokaradiyyar mu."
Shin ya yanayin tsaro a zaɓen Anambra?
Idimogu ya ƙara da jinjina ga shugaban ƙasa kan yadda aka tabbatar da tsaro a zaɓen gwamnan Anambra, wanda a cewarsa an kammala cikin kwanciyar hankali.
Hakanan ya nuna jin daɗinsa kan matakin ɗage dokar zaman gida da haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta yi lokacin zaɓen.
Ya kuma roki sabon gwamnan da ya samu nasara, Farfesa Chukwuma Soludo, wanda tsohon gwamnan CBN ne, ya yi amfani da basirarsa wajen inganta rayuwar mutanen Anambra.
INEC ta cancanci yabo
Idimogu ya shawarci hukumar zabe INEC ta ƙara inganci a shirinta, musamman sabuwar na'urar zaɓe da ta samar BVAS.
"Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta cancani yabo domin ta yi abinda ya dace duk da ƙalubalen da ta sha fama da su a Anambra."
INEC ta sanar da ɗan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APGA, Farfesa Chukwuma Soludo, a matsayin wanda ya lashe zaɓe.
A wani labarin kuma Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika
Kwamandan rundunar NSCDC yace an gayyaci wani babban mutum wanda ake zargin yana da alaka da ɗaya daga cikin waɗanda aka kama.
Rahoto ya nuna cewa ɗaya daga cikin yan bindigan da aka kama ne ya fallasa sunan sanannen mutumin wanda ke ɗaukar nauyin su.
Asali: Legit.ng