Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna
- Dan takarar gwamna a jihar Anambra a jam'iyyar PDP, Valentine Ozigbo ya taya takwaransa na APGA murnar lashe zabe
- Jam'iyyar APGA ce ta lashe zaben gwamnan jihar Anambra, inda ta yi nasara da kuri'u sama da duba dari
- Shugaba Buhari shi ma ya taya Soludo murna bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana shi yayi nasara
Anambra - Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Valentine Ozigbo, a ranar Laraba ya amince da shan kaye tare da taya dan takarar jam’iyyar APGA, Chukwuma Soludo murnar lashe zabe, Punch ta ruwaito.
Soludo mai shekaru 61 ya samu nasara da kuri’u 112,229 inda ya doke Ozigbo wanda ya samu kuri’u 53,807 da Andy Uba na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 43,285 da kuma Ifeanyi Ubah na jam'iyyar YPP da ya samu kuri'u 21,261 wanda ya zo na hudu.
Ozigbo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce:
"Yanzu na kira Farfesa Chukwuma Soludo na kuma taya shi murnar ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra, 2021. Ina yi masa fatan alheri da kuma yi masa addu'ar samun nasara."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ’yan takarar APC da YPP ba su bayyana amincersu da shan kaye a zaben ba.
A bangaren shugaban kasa Buhari, shi ma ya mika sakon taya murna da nuna goyon baya ga Soludo yayin da ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.
Zaben Anambra: Soludo ya shiga sahun su Ganduje, gwamnonin Najeriya masu PhD
Kun ji cewa, zababben gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya shiga littattafan tarihin Najeriya yayin da ya shiga jerin gwamnonin da a halin yanzu suke da digirin dgirgir (PhD).
Yawancin ‘yan siyasar Najeriya ba a san su da yin fice a fannin ilimi ba, amma labarin ya fara canjawa a cikin shekaru goma da suka gabata.
Soludo ya shiga cikin jerin fitattun kwararrun da suka yi fice a harkar kasuwanci kafin shiga cikin fafutukar siyasar Najeriya.
Asali: Legit.ng