Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

  • Wata kungiya ta nemi gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike da ya fito takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Kungiyar mai suna PDP Renaissance Movement ta ce Wike ya cancanci zama magajin shugaba Buhari domin shi mutum ne mai son hadin kan Najeriya
  • Ta kuma bayyana cewa gwamnan na jihar Ribas zai kai kasar ga matakin ci gaba idan har ya dare kujera ta daya a kasar

Calabar - Yayin da tseren shugaban kasa na 2023 ke kara daukar salo, wata kungiya mai suna PDP Renaissance Movement, ta yi kira ga gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike da ya fito takarar kujerar shugaban kasa.

Kungiyar wacce ta hada yan majalisa na jihar Cross Rivers da tsoffin kwamishinonin da suka ki bin Gwamna Ben Ayade zuwa APC, ta bayyana cewa Najeriya na bukatar mutum irin Wike wanda zai saita tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023
Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023 Hoto: Rivers state government
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a garin Calabar, daya daga cikin shugabannin kungiyar, Gab Odu Oji, ya ce kasar na bukatar sauyi a dukkan bangarori.

Ya kuma bayyana cewa Wike na da dukkanin halayyar da ake bukata domin cimma wadannan muradan, jaridar The Sun ta rahoto.

Oji ya ce:

"Kungiyar ta lura cewa Najeriya na matukar bukatar shugaba da zai ciyar da mutane gaba. Wike ya kasance dan kasa wanda ya yarda da hadin kan Najeriya kuma ya nuna hakan a lokacin annobar Sokoto.
"Wannan shine lokaci mafi muni kuma mun yi fama da matsin tattalin arziki kuma wannan shine abun da shiyya ya aikata ga kasar. Don haka, mun fito domin gyara wannan kuskure ta hanyar kawo Wike a matsayin maceci."

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Da yake magana kan mulkin karba-karba, Moses Onor ya ce:

"Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun hadu sannan sun watsar da tsarin karba-karba don haka wannan shine matsayin jam'iyyar kuma mun yi na'am da shi."

Ya ce kungiyar na ra'ayin mutum wanda ke da irin halaye da manufar gwamnan na jihar Ribas, kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Post.

Gwamna Tambuwal ya bayyana shirin da Jam’iyyar PDP take yi a game da zaben 2023

A wani labarin, shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP na kasa, Aminu Waziri Tambuwal, yace PDP na bakin kokarinta na komawa kan mulki a 2023.

Punch ta rahoto gwamnan na jihar Sokoto yana wannan jawabi a lokacin da ya zanta da manema labarai a gidan tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko.

Da yake jawabi a garin Ondo a ranar 28 ga watan Oktoba, 2021, Aminu Waziri Tambuwal yace jam’iyyar PDP ta dage wajen ganin ta sake rike Najeriya.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng