KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2

KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2

A ranar Asabar ne aka kada kuri'a a zaben gwamna na jihar Anambra, amma aka samu tsaiko a wasu yankuna saboda wasu dalilai.

An sanya ranar Talata a matsayin ranar da za a ci gaba da kada kuri'a a karamar hukumar Ihiala, wanda aka ce ba a aminta da zaben yankin ba.

Ku biyo don jin yadda za ta kaya a ci gaba da zaben gwamnan, wanda zai zo muku kai tsaye daga majiyoyi masu tushe.

Kamar yadda aka yi tsammani, an dasa jami’an tsaro sosai a hedikwatar karamar hukumar Ihiala inda INEC ke shirye-shiryen sake zaben na yau, inji rahoton The Cable.

KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2
Asali: UGC

An fara tantancewa da kirga kuri'a a rumfunan zabe

Rumfar zabe ta Uzokwa, tuni an fara tantancewa da kidayar kuri'u.

Jama’a sun sa ido sosai wajen tantancewa da kidayar kuri’u a Uzokwa.

Jami'an INEC suna yiwa katin zabe mara amfani alama.

Zabe ya fara zuwa karshe

Zuwa karfe 3:00 na rana kusan dukkan masu kaɗa kuri'a a runfunan zaɓen gundumar Uzokwa 3 sun jefa kuri'un su.

Wakilin jam'iyyar APGA, Arinze Chukwu, ya shaida wa The Cable cewa zaɓe na gudana cikin inganci da sahihanci.

Zaben Anambra
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yan sanda sun fara sintiri a jirgi mai saukar Angulu

Kallo ya koma sama, yayin da jirgin jami'an yan sanda ya fara yawon duba halin da ake ciki a karamar hukumar Ihiala yayin da zabe ya kankama kusan ko ina.

Zaben wanda ya gamu da cikas na rashin fara wa kamar yadda aka tsara, yana cigaba da tafiya ba tare da samun tangarɗan na'urar BVAS ba.

Jirgin yan sanda
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mataimakin kakakin majalisar dokokin Anambra ya kaɗa kuri'arsa

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Patrick Agbodike, ya jefa kuri'arsa a PU10, RA 20, Mbosi.

An fara kaɗa kuri'a a wurin da misalin ƙarfe 12:00 na rana bayan dogon jira, kuma na'urar BVAS tana aiki yadda ya kamata.

Waiwaye: Yadda zabe ya kaya da adadin kuri'un 'yan takara

A halin yanzu, ana ci gaba da kada kuri'u a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra. Ga kadan daga sakamakon da aka tattara na sauran kananan hukumomi zuwa yanzu.

1. Chukwuma Soludo na APGA ya samu kuri’u 103,946

2. Valentine Ozigbo na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 51,322

3. Andy Uba, dan takarar jam’iyyar APC ya samu kuri’u 42,942

An fara kada kuri'a, ya zuwa yanzu babu wata damuwa

A karshe, an fara kada kuri’a a sassan mazabun Uzokwa. Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Sai dai, rahotanni sun ce an ji karar harbi a wani yanki.

Daga karshe: Jami'an INEC sun isa rumfar zabe bayan dogon jira, masu kada kuri'a na jira

Daga karshe dai jami’an hukumar zabe ta INEC sun isa Uzokwa Ward 3, a daidai lokacin da masu kada kuri’a ke zaman jira.

Kamar yadda aka yi a ranar Asabar din da ta gabata, masu zabe, wadanda galibinsu tsoffi ne, sun tsaya daram a lokacin da INEC ta dira a Uzokwa Ward 3.

Masu kada kuri'a na cikin shirin ko ta kwana yayin da jami'ai ke shirin fara aikinsu a Uzokwa Ward 3 da ke a karamar hukumar Ihiala.

Babu jami'in INEC ko daya a gudumar Uzokwa wurin karfe 11: 53

Har zuwa karfe 11: 53 na safe, babu jami'in hukumar zabe mai zaman kan ta ko daya da aka gani a makarantar sakandaren 'yan mata da ke Abobot, gunduma ta 3 da ke Ihiala inda akwai sama da rumfunan zabe ashirin.

Masu kada kuri'a sun taru a makarantar suna jiran isowar jami'an

KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ba a fara tantance masu kada kuri'a ba har karfe 11:05 am

Da karfe 11:05 am na safiyar Talata, 9 ga Nuwamba, ba a fara tantance masu kada kuri'a ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Daidai 11:30am, an fara raba kayayyakin zabe a sakateriyar karamar hukumar Ihiala ta jihar.

Sojoji sun kori jigon APGA, Victor Umeh, daga Ihiala HQ

Sojoji sun hana jigon jam'iyyar APGA, Victor Omeh, shiga hedkwatar Ihiala, wanda ya dira wurin tare da wasu mambobin jam'iyyarsa.

"Bai kamata ka zo nan ba," Kwamandan Soji GOC na runduna ta 82 ke nanata wa Omeh, yayin da yake cewa, "Na zo nan ne domin tabbatar da komai na tafiya dai-dai."

Victor Omeh
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ma'aikata sun tattaru suna jiran a raba musu kayan zaɓe

Da misalin karfe 10:00 na safe ya kamata a fara zaɓen kamar yadda INEC ta sanar amma a halin yanzun an samu tsaiko.

Tuni ma'aikatan wucin gadi da suka hada da matasa yan bautar ƙasa suka taru a harabar hedkwatar karamar hukumar Ihiala suna jiran a basu kayan aiki.

Ma'aikatan wucin gadi
KAI TSAYE: Ana cigaba da zaben Anambra bayan tsaikon kwana 2 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.