Shugaban APGA dake gab da lashe zaben Gwamnan Anambra ya magantu kan sakamako

Shugaban APGA dake gab da lashe zaben Gwamnan Anambra ya magantu kan sakamako

  • Shugaban jam'iyyar APGA, Chief Victor Oye, yace Najeriya ta kai matsayin da zata gudanar da zaɓe ta na'ura kuma a tura sakamako
  • A cewarsa zaɓen Anambra shine babban misali kuma za'a iya faɗaɗa irin haka zuwa dukkan faɗin Najeriya
  • Ya kara da cewa zaben Anambra da aka gudanar ba shi da makusa domin an yi komai cikin zaman lafiya

Anambra - Shugabam jam'iyyar APGA, Chief Victor Oye, yace yana da yakini Najeriya zata iya gudanar da zabe ta na'ura kuma a tura sakamako ta na'ura.

Channels tv tace Oye ya yi wannan furuci ne yayin da ake cigaba da karban sakamakon zaɓen gwamnan daga kananan hukumomin jihar Anambra ranar Lahadi.

Na'urar BVAS
Shugaban APGA dake gaba da lashe zaben Gwamnan Anambra ya magantu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yace:

"Tsarin zaɓe ta na'ura ya yi aiki sosai, akwai bukatar INEC ta sake gyara shi, amma Najeriya ta kai matsayin da zata gudanar da zabe ta na'ura."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

"Zamu iya kaɗa kuri'ar mu ta na'ura, wannan shine babban darasin da muka koya a wannan zaɓen, abu ne mai sauki gudanar da zaɓe da tura zaɓe ta na'ura."

Shin ya aka gudanar da zaɓe a Anambra?

Da yake magana kan zaben da aka gudanar ranar Asabar, Oyo ya bayyana cewa an yi komai cikin zaman lafiya, kuma za'a iya yin kwatankwacin haka a faɗin Najeriya.

"Babu wani zaɓe da zai fi wannan kwanciyar hankali, shine mafi kyaun zaɓe da muka taba yi a jihar nan. Zan iya cewa Najeriya zata iya tsaftataccen zabe fiye da haka."

Shin yan siyasa sun siya kuri'u?

A rahoton da suka fitar ranar Lahadi kan zaɓen, masu sanya ido sun bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

A cewar kungiyar babban nakasun da aka samu a zaben shine siyan kuri'u wanda ya kama daga N1,000 zuwa N6,000.

A wasu runfunan zaɓen an gudanar da haka a sirrince, yayin da wasu wuraren kuma aka rinka siyan kuri'u kowa na gani ba tare da jami'an tsaro sun hana ba, cewar masu sanya ido.

A wani labarin kuma Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262