Rikicin APC ya tsananta: Gwamna Buni ya dakatar da kwamitin zaɓen shugabannin APC na wannan jihar

Rikicin APC ya tsananta: Gwamna Buni ya dakatar da kwamitin zaɓen shugabannin APC na wannan jihar

  • Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a Zamfara ya sake ɗaukar sabon babi yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta dakatar da kwamitin zaɓe
  • Gwamna Mai Mala Buni, ya ɗauki matakim dakatar da kwamitin gudanar da zaɓen gundumomi a jihar bisa wasu dalilai
  • Tuni kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa ya aike da sakon dakatarwa ga shugaban kwamitin, Ibrahim Kabir Masari

Abuja - Alamun dake kara bayyana na nuni da cewa babu ranar kawo ƙarshen rikicin cikin gida na jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Zamfara.

Tribune Online ta ruwaito cewa sakateriyar jam'iyyar APC ta ƙasa ta sake dakatar da kwamitin gudanar da gangamin taron APC na gundumomi a jihar Zamfara.

A wani memo mai kwanan watan 5 ga watan Nuwamba, wanda ke ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin rikon kwarya na ƙasa, Sanata James John, yana ɗauke da takardar dakatar da kwamitin gudanar da gangamin zaben.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya sallami shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Rikicin APC ya kara tsananta
Rikicin APC ya kara tsananta: Gwamna Buni ya dakatar da zababbun shugabannin APC na wannan jihar Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Takardan dai an sanya adireshin shugaban kwamitin gudanar da zaɓen gundumomi a Zamfara, Ibrahim Kabir Masari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me takardan dakatarwan da ƙunsa?

Wani sashin takaradar yace:

"Shugaban kwamitin rikon kwarya kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bada umarnin dakatar da kwamitin gudanar da zaɓen shugabannin APC a matakin gundumomi na jahar Zamfara."
"APC ta ɗauki wannan matakin ne domin sake nazari da kuma shawarwari wajen ganin an gudanar da gangamin tarukan cikin kwanciyar hankali."
"Shugaban APC na ƙasa yana fatan waɗan da abun ya shafa zasu fahimci abinda ya jawo haka, yayin da ake cigaba da kokarin nemo hanyoyin haɗin kai a cikin gida."

Daga ƙarshe sakon ya umarci shugaban kwamitin da ya sanar da sauran mambobin kwamitinsa matakin da aka ɗauka.

A wani labarin kuma kun ji Yadda wasu fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar INEC ta fara rabon kayan zaben gwamnan jihar Anambra

Rahoto ya bayyana cewa ma'aikatan ne suka nemi barin cibiyar tattara sakamakon gundumar Oko II domin su koma ofishin INEC .

Lamarin ya saitu ne bayan sojoji sun shiga lamarin, inda suka kwashe kayan aikin zabe masu muhimmanci zuwa ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262