Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

  • Gwamnatin jihar Anambra ta karyata rahoton da ke yawo na cewa mutane na tururuwan barin jihar yayin da ake zaben gwamna
  • Rahoton dai ya yi ikirarin cewa mutane na barin Anambra saboda tsoron barkewar rikicin siyasa a yayin zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba
  • Kwamishinan labarai da wayar da kan jama'a na jihar, Mista Don Adinuba, ya ce mutane sun koma wuraren da suka yi rijistar zabe ne domin samun damar kada kuri'a

Anambra - Kwamishinan labarai da wayar da kan jama'a na jihar Anambra, Mista Don Adinuba, ya ce rahoton da ke yawo na cewa mutane na tururuwan barin jihar yayin da ake zaben gwamna karya ne.

Adinuba ya bayyana cewa maimakon haka, mutane na shigowa cikin jihar kwansu da kwarkwatarsu, musamman wadanda suka cancanci yin zabe domin shiga sahun masu kada kuri'a a zaben gwamnan wanda ke gudana a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna

Zaben 2021: Karya ne masu zabe basu yi tururuwan barin gari ba - Kwamishina
Zaben 2021: Karya ne masu zabe basu yi tururuwan barin gari ba - Kwamishina
Asali: UGC

Ya magantu a kan lamarin ne a cikin wata sanarwa, wanda aka aike wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a safiyar ranar Asabar a garin Awka, babbar birnin jihar, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana cewa an ja hankalin gwamnatin jihar a kan rahoton labaran wanda ke ikirarin cewa mutane na barin Anambra saboda tsoron rikicin siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya karyata rahoton, inda ya ce mutanen Anambra basu nuna tsoron yiwuwar barkewar kowani rikici ba kafin da bayan zabe.

Ya ce:

"Mutanenmu sun san tushensu, don haka yawanci suna yin rajistar zabe ne a jihar ko da kuwa suna zama da aiki a wani wuri ne."

Ya bayyana cewa mutane da dama da ke aiki a birane a Anambra, su kan yi rijistansu a mahaifarsu sannan da hutun aiki da aka bayar a ranar Alhamis da Juma'a, da dama sun tafi mahaifarsu don kada kuri'a.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa mutane da dama sun bar biranen ne a cikin sa'o'i 24 da suka gabata zuwa garuruwansu inda suka zaba don jefa kuri'arsu, rahoton The Guardian.

Ya kara da cewa:

"Don haka ba daidai bane wata kafar yada labarai ta yi ikirarin cewa mutanen Anambra na barin jihar don tsoron barkewar rikicin siyasa.
"Idan da dan jaridar da ya rubuta rahoton yana ikirarin ana gudun hijira ya damu da neman karin haske ko bayani kan ci gaban, da bai rubuta rahoton mai rikitarwa ba.
“Abin mamaki ne a ce wani dan jarida zai iya gabatar da irin wannan rahoto ba tare da ya tuntubi gwamnati ba, duk da bude kofa da wannan gwamnati ta yi ga kafafen yada labarai.”

Zaben Gwamnan Anambra: Dan takaran APGA ya ce takaran APC mai garkuwa da mutane ne

A wani labarin, dan takaran gwamnan jihar Anambra karkashin jam'iyyar APGA, Charles Soludo, ya tuhumi abokin hamayyarsa, Andy Uba na APC, da laifin amfani da kwalin bogi.

Kara karanta wannan

Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi

Hakazalika ya zargeshi da garkuwa da mutane, musamman na tsohon gwamnan jihar Chris Ngige.

Soludo ya bayyana hakan ne lokacin da yan takaran suka kara da juna a taron muhawaran da Arise News TV ta shirya kuma Legit.ng ta shaida ranar Litinin, 1 ga Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng