Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

  • Domin dinke barakar da ta kunno a jam'iyyar APC a jihar Oyo, Buni zai gana da masu ruwa da tsaki
  • Ya gayyaci jiga-jigan jam'iyyar APC na Oyo ne bayan da aka Sami baraka bayan taron gangamin jihar
  • Ance gwamna Mai Mala Buni zai shiga tsakani ne domin wanzar da zaman lafiya a jam'iyyar APC

Abuja - A karshe dai kwamitin tsare-tsare na taron gangamin jam’iyyar APC ya dauki matakin shiga tsakani a rikicin da ya biyo bayan taron majalisar jihar da aka gudanar a karshen makon da ya gabata a jihar Oyo.

Wata majiyar jam’iyyar ta shaida wa Nigerian Tribune a ranar Larabar da ta gabata cewa gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni, ya gayyaci jiga-jigan jam’iyyar zuwa wata ganawa da aka shirya yi a yau.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo
Mai Mala Buni, Gwamnan jihar Yobe | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

A karshen taron gangamin da aka gudanar a filin wasa na Obafemi Awolowo, tsohon kwamishinan filaye da gidaje Isaac Omodewu ya zama shugaban APC na jihar Oyo.

Sai dai kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar a jihar sun kauracewa taron da aka dage sau biyu.

Daga cikin wadanda suka kaurace wa taron har da ministan matasa da raya wasanni, Mista Sunday Dare da shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Farfesa Adeolu Akande.

Hakazalika da Sanata Ayoade Adeseun, Sanata Olufemi Lanlehin; dan takarar gwamna na 2019 a jihar, Mista Adebayo Adelabu; tsohon sakataren gwamnatin jihar, Sharafadeen Alli; Dr Azeez Adeduntan da Mr Joseph Tegbe.

Sauran sun hada da Alhaji Fatai Ibikunle, Niyi Adeagbo, Mrs Folake Oshinowo, Gbenga Olayemi, Kola Olabiyi, Wasiu Owolabi, Ambali Abiodun da Olalekan Kazeem, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

Wata majiyar jam’iyyar ta shaida cewa tsohon gwamnan jihar Oyo kuma jigo a jam’iyyar, Cif Adebayo Alao-Akala, ya gana da gwamna Buni a gidansa na kashin kansa da ke Abuja a daren jiya, gabanin ganawar da za a yi na yau da masu ruwa da tsaki a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar The Guardian a jiya, shugaban kwamitin riko na jihar, Mista Akin Oke, ya yi watsi da rade-radin cewa jam’iyyar za ta sake gudanar da wani taron gangamin jiha a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba, 2021, kamar yadda ake yadawa.

Tsohon gwamna ya caccaki APC: Duk APC babu na gari, jam'iyyar 'yan rashawa ce

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya caccaki ayyukan jam’iyyar APC a kasar nan.

Yayin da yake bayyana ayyukan gwamnatin APC kawo yanzu, Lamido ya bayyana jam’iyya mai mulki a matsayin jam’iyya juya wacce ba ta iya samar da kyakkyawan shugabanci ga kasar nan.

Kara karanta wannan

Ana saura mako daya zabe Gwamna, yan majalisa 3 sun sauya sheka APC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.