Zaben Anambra: Yan takarar gwamna 9 sun yi kira ga sakin Nnamdi Kanu
- Gabannin zaben gwamnan jihar Anambra, yan takarar zaben su tara sun nemi gwamnatin tarayya ta saki shugaban kungiyar yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu
- Sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannunsu
- Yan takarar sun kuma bukaci FG ta janye sojoji daga kudu maso gabas domin dakile fargabar da ake ciki a yankin
Anambra - Yan takarar zaben gwamnan jihar Anambra su tara sun yi kira ga sakin shugaban kungiyar yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.
Wannan na zuwa ne yayin da suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta janye sojoji daga yankin na arewa maso gabas a kokarin dakile fargabar da ke yankin, jaridar Punch ta rahoto.
Jaridar The Cable ta kuma rahoto cewa yan takarar sun bayyana matsayinsu ne a wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannun Ben Etiaba, tdan takarar AA; Charles Soludo, APGA; Obinna Uzoh, SDP; Akachukwu Nwankpo, ADC.
Sauran wadanda suka sa hannu sune Onyejegbu Okwudili, APM; Ifeanyi Uba, YPP; Andy Uba, APC; Nnamdi Nnawuo, PRP da Obiora Okonkwo of the ZLP.
Yan takarar sun nuna jin dadinsu a kan damuwar da majalisar sarakunan gargajiya na kudu maso gabas da wakilan fastocin Igbo suka nuna game da fargabar da ke tattare da tashe-tashen hankula a yankin.
Sun ce:
"Mu, yan takarar zaben gwamnan jihar Anambra mai zuwa, muna muradin rashin tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya a duk tsawon lokacin zaben da ma bayan zaben.
"Muna kira ga dukkanin magoya bayanmu da sauran masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen aiwatar da wadannan manufofin tare da kaucewa duk wani abu da zai kawo cikas ga zaben.
“Domin dakile duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zabe mai zuwa, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki Mazi Nnamdi Kanu ga Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kudu maso Gabas da kuma wakilan manyan fastocin Igbo.
"Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta daukar matakai don janye sojoji daga yankin kudu maso gabas da dakile fargaba, fadace-fadace da zubar da jini mara iyaka tsakanin jami’an tsaro da matasanmu.”
Sun kuma yi kira ga IPOB da su guji aikata abubuwan da zai kawo cikas ga gudanar da zabe cikin lumana.
"Muna umurtan yan IPOB da kada su yi abun da zai kawo cikas ga gudanarwar zaben gwamnan jihar Anambra cikin lumana sannan su soke umurnin zaman gida, domin wadannan sun rigada sun haifar da wahala ga mutanenmu.
"Muna kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, rundunar soji, da sauran hukumomin tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki da su aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata daidai da doka sannan su yi adalci a gudanarwarsu."
A dage zaben gwamnan Anambra domin kare rayuka – Babban fasto ga FG
A gefe guda, mun ji cewa yan kwanaki kafin zaben gwamnan Anambra, shahararren faston nan na Najeriya, Bishop Abraham Udeh, ya ce ya zama dole hukumomin da abun ya shafa su gaggauta dakatar da zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba domin kare rayuka.
Bishop Udeh wanda aka fi sani da Fire By Fire ya ce ya ga jini na zuba tamkar kogi a jihar inda ake ta kururuwa da kuka a yankunan Anambra da dama.
Ya dage cewa mafita kwaya daya shine a kara watanni shida kafin ayi zaben, jaridar The Sun ta rahoto.
Asali: Legit.ng