Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC
- Sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan zabansa da aka yi a ranar Asabar yayin taron gangamin PDP
- Ya shaidawa matasa cewa, wannan nasara ce ga daukacin matasan PDP da na Najeriya baki daya don kawo ci gaba
- A bangare guda, ya ci alwashin ba zai ba dattawan jam'iyyar PDP kunya ba bisa yarda dashi da suka yi
Kaduna - Zababben shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa, Muhammed Kadade Suleiman, ya ce nasararsa alama ce mai nuna jam’iyyar na damawa da matasa da sanya su cikin mukaman shugabancin jam’iyyar gabanin 2023.
Ya yi kira ga matasan Najeriya da su shiga jam’iyyar PDP domin ceto kasar nan da kuma ceto makomarsu daga halaka, Daily Trust ta ruwaito.
Kadade, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce kofarsa a bude take ga kowa, don ba da shawara, gudummawa da goyon baya.
Ya ce, duk wannan zai yi ne domin gudanar da ayyukansa kamar yadda ya yi alkawarin aiki don tabbatar da burin PDP na komawa kan karagar mulki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
“A karkashin jagorancin sabon shugabanmu da aka zaba, Dr Iyorchia Ayu, ni da sauran zababbun mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC), za mu yi aiki tukuru don mayar da PDP zuwa Aso Rock a 2023."
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, suna sane da irin kalubalen da matasa ke fuskanta a halin yanzu da rashin tafiyar da gwamnati da APC ke fuskanta, inda ya kara da cewa:
"Ko kun zabe ni ko ba ku zabe ni ba, ko kun goyi bayana ko ba ku ba goyi bayana ba, ina so in tabbatar muku cewa wannan nasara ce ba ga ni kadai ba, nasara ce ga daukacin jam'iyyar PDP da kuma matasan Najeriya."
Ya sha alwashin ba zai ba wa dattawan jam’iyyar kunya ba da suka ba shi damar yin aiki a jam'iyyar.
Mohammad Kadede Suleiman, matashi ne mai shekaru 25
Rahotanni da muke samu daga jaridar Punch sun bayyana cewa, wani dan shekara 25 ne ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa.
An zabi Mohammad Kadade Suleiman mai shekaru 25 a matsayin shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa. An zabe shi ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka kammala a Abuja.
A ranar Asabar ne aka gudunar da taron gangamin PDP, taron da ya sami halartar jiga-jigan jam'iyyar ta PDP daga sassa daban-daban na kasar nan.
Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya
A baya, daga cikin bukukuwan da suka gudana a taron gangamin PDP, an kada kuri'u na kujeru daban-daban na shugabancin jam'iyyar ta adawa.
Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya cewa, PDP ta yi sabbin kujerun shugabancin jam'iyyar, inda aka lissafo wasu jami'an PDP 21 da suka yi nasara a zaben.
Bayan zaben, an samu cece-kuce daga bangarori daban-daban na 'yan Najeriya, inda jama'a da yawa suka bayyana ra'ayoyinsu game da hakan.
Asali: Legit.ng